EFCC: An fara zargin Hukuma da yi wa manyan Ma’aikata cin layi a aiki
Bincike na musamman da jaridar The Cable ta yi, ya nuna cewa akwai zargin cin layi da ake yi a hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin Najeriya zagon-kasa.
Jaridar ta ce an tura wasu daga cikin jami’an hukumar EFCC su rike manyan ofisoshi na shiyyoyi da ake da su a fadin kasar nan duk da cewa akwai wadanda su ka sha gabansu.
Wannan mataki da EFCC ta dauka bai yi wa manyan ma’aikatan hukumar dadi ba. Abin da hakan ya ke nufi shi ne za a samu jami’an da ke daukar umarni daga wurin yaransu.
Sabon mukaddashin shugaban EFCC na kasa, Mohammed Umar ne ya yi nadin mukaman da ya bar wasu jami’ai su na ta faman guna-guni kamar yadda rahoton ya bayyana.
A wata takarda da ta fito daga hukumar EFCC ta shiga hannun jaridar, an ga cewa Mohammed Umar ya sauyawa ma’aikata 37 wurin aiki, daga ciki akwai manyan jami’ai 20.
Binciken da aka yi, ya nuna cewa wasu daga cikin wadannan ma’aikata 20 da aka zaba za su rike ofisoshin shiyyoyi ne, yayin da wasunsu kuma za su zama mataimakansu.
Sabon shugaban na EFCC, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne kuma darekta kafin yanzu.
Mafi yawan wadanda aka ba wannan aiki su na kan mukamin PDS, DCDS, CSP da kuma ACP ne. PDS shi ne mataki na babban mai bincike, DCDS shi ne mai bi masa a aiki.
Umar ya umarci wadanda aka ba mukami su yi maza su soma aiki ba tare da jiran wata-wata ba.
Wani ma’aikacin hukumar EFCC ya shaidawa jaridar a boye cewa wannan nadin mukamai da aka yi kwanan nan, ya sabawa yadda aka san hukumar kasar da rabon aiki.
“Sababbin nadin mukaman da aka yi ya fito kwanan nan, sai a dauki ma’aikacin da ke kan matakin aiki na 12 ko 13, ace zai jagoranci jami’in da ya kai mataki na 16 a babban ofis.”
Majiyar ya koka da yadda ake so babba ya dauki umarni wurin yaronsa. Ya ce: “A bangaren shari’a, an daina aiki. Dole sai an shawo kan wannan matsala, babu adalci a haka.”
KU KARANTA: Magu ya kare kansa daga zargin facaka da dukiyar Gwamnati
Jami’in ya ke cewa: “EFCC ce kawai hukumar da babba ya ke daukar umarni daga karami.”
Ga jerin jami’an da aka yi wa sauyin wurin-aiki:
1. Baba Mallam
2. Daniel O
3. Itam Obono
4. Babalola Johnson
5. Hadjia Mohammed
6. Chukkol Abdulkareem
7. Onwukwe Obiora
8. Mukhtar Bello
9. Ozugha Innocent
10. Edeh Uchenna
11. Oseni Kazeem
12. Bawa Kaltungo
13. Kumo Modibbo
14. Ringim Hauwa
15. Akogwu Eleojo
16. Amusan Kolawole
17. Abdullahi Lana
18. Adebayo Adeniyi
19. Oshodi Johnson
20. Akinroyeje Toyosi
21. Mualledi Dogondaji
22. Bawa Saidu
23. Aliyu Nuhu
24. Abdulrasheed Ahmed
25. Usman Muktar
26. Ahuchogu Austen
27. Ishaya Dauda
28. Usman Sambo
29. Ajani Aminat
30. Mohammed Sanusi
31. Thomas Kadiri
32. Abdullahi Sanusi
33. Ahmad Sabir
34. Rilwan Hamzat
35. Bamisaye Oyedele
36. Ahmed Usman
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng