'Yajin aikin da mu ka shiga zai fara aiki da zarar an bude jami'o'i' - NASU da SSANU

'Yajin aikin da mu ka shiga zai fara aiki da zarar an bude jami'o'i' - NASU da SSANU

Wani kwamitin hadin gwuiwa (JAC) tsakanin kungiyar kananan ma'aikatan jami'o'i (NASU) da kungiyar manyan malaman jami'o'i (SSANU) ya sanar da shigarsu yajin aikin sai baba ta gani daga ranar da aka bude makarantu.

Shugaban kungiyar SSANU ta kasa, kwamred Samson Ugwoke, ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai da yammacin ranar Alhamis bayan kammala taron JAC a Abuja.

Ya bayyana cewa NASU da SSANU sun yanke shawarar shiga yajin aiki sakamakon fuskantar matsin lamba daga wurin shugabannin kungiyoyin.

"Mun shiga yajin aiki sai baba ta gani wanda zai fara daga ranar da gwamnati ta amince a bude makarantu bayan janye dokar kulle da aka saka sakamakon barkewar annobar korona.

'Yajin aikin da mu ka shiga zai fara aiki da zarar an bude jami'o'i' - NASU da SSANU
kwamred Samson Ugwoke yayin ganawa da manema labarai a Abuja
Asali: UGC

"Kungiyoyinmu sun kasance ma su juriya da hakuri da halayen gwamnati, ba za mu yi rigima da gwamnati ba duk da tura ta kai bango, a saboda haka mu ka yanke shawarar shiga yajin aiki.

"Idan ya kasance har an bude makarantu ba tare da biyan bukatunmu ba, babu sauran wani uzuri kuma babu abinda zai hana yajin aikinmu," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Faifan bidiyo:

Sannan ya cigaba da cewa; "an bamu tabbacin cewa za a saka mana dukkan alawus dinmu a cikin sabon tsarin biyan albashin ma'aikatan gwamnatin tarayya (IPPIS), amma har yanzu hakan ta gagara."

"Sakamu a cikin tsarin ya zama tamkar annoba, kamar tsallen kwado daga cikin wuta zuwa kaskon suya. Biyan albashinmu da sauran hakkokinmu ya shiga mawuyacin hali."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel