Borno ta dauki 35% na kashe-kashen da aka yi a rabin shekarar bana
Alkaluman da Nigeria Security Tracker da CFR ta fitar ya bayyana cewa mutane sama da 5, 600 su ka mutu a watanni shida na farkon shekarar nan.
Kamfanin StatiSense da su ka saba tara alkaluma na kasashen Duniya sun ce an rasa wadannan mutane a Najeriya ne daga farkon Junairu zuwa watan Yuli.
Kamar yadda alkaluman su ka nuna, jihar Borno ta dauki akalla 35% na kason kashe-kashen da aka yi a wannan lokaci. Jihar ta rasa rayukan fiye da mutum 2, 000.
Legit.ng ta lura cewa jihohi 12 na farko da aka fi fama da kashe-kashe, duk sun fito ne daga yankin Arewacin kasar.
Jihohin Kudancin Najeriya biyar kacal ne su ka fito a cikin sahun 20 na farko. Jihohin su ne: Delta, Ribas, Edo, Bayelsa da kuma Kuros-Riba inda aka rasa rayuka 215.
A shekarar nan babu jihar da ba a samu kashe-kashe ba. Jihar farko da ta fito a wannan mummunan sahu daga Kudancin Najeriya ita ce Delta a yankin Neja-Delta.
KU KARANTA: Sanatoci sun dage a kan maganar sauke Hafsun Sojojin Najeriya
Jihar da ta samu karancin adadi ita ce Kebbi inda mutum daya aka rasa a sanadiyyar kashe-kashe a tsawon watanni shida.
Sauran fitattun jihohin da ba a samu kashe-kashe su ne Bauchi, Kwara, Jigawa, Kano da birnin tarayya Abuja. A Kano rayuka biyu kacal aka rasa zuwa yanzu.
Ga yadda jerin ya ke:
Borno: 2,038
Kaduna: 730
Zamfara: 727
Katsina: 565
Benue: 161
Yobe: 149
Taraba: 135
Niger: 130
Adamawa: 119
Sokoto: 111
Filato: 110
Kogi: 88
Delta: 67
Ribas: 51
Edo: 48
Legass: 43
Oyo: 32
Anambra: 30
Bayelsa: 30
Kuros Riba: 30
Ebonyi: 28
Nassarawa: 27
Ondo: 24
Ogun: 23
Habuja: 20
Imo: 16
Abia: 12
Akwa Ibom: 11
Bauchi: 11
Kwara: 8
Osun: 7
Enugu: 6
Jigawa: 6
Ekiti: 4
Kano: 2
Kebbi: 1
(Alkaluma daga: Nigeria Security Tracker / CFR)
Kafin yanzu kun ji cewa Shugaba Hassan Rouhani zai taimakawa kasar Lebanon da kayan magani bayan abin da ya faru a garin Bierut.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng