Kada ku raba kan ahlinmu – Iyalan Obaseki sun karyata goyon bayan Ize-Iyamu

Kada ku raba kan ahlinmu – Iyalan Obaseki sun karyata goyon bayan Ize-Iyamu

- An shiga halin fargaba a Edo yayinda zaben gwamnan jihar ke kara gabatowa

- Ahlin gidan Gwamna Godwin Obaseki sun karyata goyon bayan Fasto Osagie Ize-Iyamu

- Kakakin ahlin, Oyuki Gaius-Obaseki Jr, ya ce wadanda suka marawa dan takarar APC baya ba da yawunsu bane

‘Yan uwan Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo sun karyata batun goyon bayan Fasto Osagie Ize-Iyamu, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zabe mai zuwa.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, 5 ga watan Agusta, kakakin ahlin gidan gwamnan na Edo, Oyuki Giaus-Obaseki Jr, ya ce iyalan ba za su nade hannu suna kallo ba yayinda wasu ke kokarin kawo baraka a tsakaninsu.

Gaius-Obaseki ya kara da cewa iyalan sun amince da daukar mataki kan wadanda suka yi masu kagen, inda suka kara da cewar wadanda suka marawa abokin adawar dansu baya sun ji kunya.

Kada ku tarwatsa kan ahlinmu – Iyalan Obaseki sun karyata goyon bayan Ize-Iyamu
Kada ku tarwatsa kan ahlinmu – Iyalan Obaseki sun karyata goyon bayan Ize-Iyamu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

“Mun yi Allah wadai da kokarin wasu na haifar da rabuwar kai a ahlinmu don wani buri na kansu. Kuma mun amince da daukar mataki kan wadannan mutane,” in ji Obaseki Jr.

“A matsayinmu na ‘yan uwan juna, muna da wasu ‘ya’yan da suka bar hanya, ba za mu kore su ba. Ba za mu sallama su ba.

“Wadannan mutane (wadanda suka marawa Ize-Iyamu baya) ba su samu izinin goyon bayan wani a madadin iyalan Obaseki ba kuma ba su ke wakiltanmu ba. Sun je don kansu ne tunda basu da kunya,” Obaseki Jr ya kara da cewa.

Za a gudanar da zaben gwamnan Edo a watan Satumba, inda manyan jam’iyyu biyu na APC da PDP za su gwabza.

KU KARANTA KUMA: Kwamitin Salami ya yi alkawarin sauraron Magu, ya yi watsi da wata bukatar da ya mika

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu mambobin jam'iyyar PDP karkashin inuwar wata kungiyar masu ruwa da tsaki ta jihar Edo, ta mika korafi ga hukumar yaki da rashawa.

'Ya'yan jam'iyyar sun nemi hukumar da ta binciki Gwamna Godwin Obaseki a kan zarginsa da ake da waskar da wasu makuden kudade.

Sun bukaci da a binciki gwamnan a kan wata kwangilar da ya bai wa kamfaninsa mai suna Afrilnvest Ltd.

Amma mai bada shawara ga Obaseki a fannin yada labarai, Crusoe Osagie, ya ce wannan korafin sharri ne wanda jam'iyyar APC ke shiryawa don bata sunan gwamnan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel