Yanzu nan: Sanata Gbenga Ashafa zai rike Hukumar gidajen Gwamnati na kasa

Yanzu nan: Sanata Gbenga Ashafa zai rike Hukumar gidajen Gwamnati na kasa

- Gbenga Ashafa ya zama Shugaban hukumar gidaje na FHA a Najeriya

- Gwamnatin Legas ta tabbatar da wannan mukami da aka ba Sanata Ashafa

- Shi ma Abdulmumin Jibrin wanda ya rasa kujerarsa ya samu mukami

Mun samu labari cewa Gbenga Ashafa na Legas ya samu mukami da gwamnatin tarayyar Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Gbenga Bareehu Ashafa a matsayin babban darektan hukumar gidaje na kasa FHA.

Hadimin gwamnan jihar Legas, Mista Gawat Jubril shi ne ya bada sanarwar wannan mukami da aka ba tsohon Sanatansa a ranar Laraba.

Jubril wanda ya ke taimakawa gwamna Babajide Sanwo-Olu a kan kafafen sadarwa na zamani ya bayyana wannan ne a shafinsa na Twitter.

Da ya ke bada sanawar a ranar 5 ga watan Agusta, 2020, Gawat Jubril ya ce Gbenga Ashafa zai shiga ofis ne ba tare da wata-wata ba.

Tsohon Sanatan na Legas ta gabas zai rike hukumar FHA a matsayin babban darekta na kasa.

KU KARANTA: Hon. Jibrin ya samu mukami a Gwamnatin Buhari

Yanzu nan: Sanata Gbenga Ashafa zai rike Hukumar gidajen Gwamnati na kasa
Sanata Gbenga Ashafa a Majalisa Hoto: Senate
Source: UGC

Ashafa mai shekaru 65 ya wakilci mazabarsa a majalisar dattawa sau biyu daga 2011 zuwa 2019 a karkashin jam’iyyar ACN da APC.

Sanata Ashafa ba bako ba ne a irin wannan aiki, a 2001 Bola Tinubu ya nada shi Sakataren kwamitin rabon filaye na jihar Legas.

Haka zalika a 2005, Ashafa ya zama sakataren din-din-din a ma’aikatar filaye na gwamnatin jihar Legas, ya yi ritaya ne a 2010.

Sabon darektan ya yi digiri da digirgir ne a jami’ar jihar Morgan da ke Maryland da kuma jami’ar Tennessee a Knoxville, duk a Amurka.

A daidai wannan lokaci kuma an nada tsohon ‘dan majalisar Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin a matsayin darekta a hukumar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel