Ibrahim Gobir ya hakikance a kan sauya Hafsun Sojoji saboda matsalar tsaro

Ibrahim Gobir ya hakikance a kan sauya Hafsun Sojoji saboda matsalar tsaro

Shugaban kwamitin sa ido a harkar tsaro a majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir, ya ce su na nan a kan ra’ayinsu game da hafsun sojoji.

Ibrahim Abdullahi Gobir mai wakiltar Sokoto ta gabas ya bayyana cewa majalisar dattawa ba ta sauka daga matsayar da ta hau na sauya hafsun sojoji ba.

Jaridar This Day ta ce Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ya yi wannan bayani ne a ranar Talata a garin Sokoto, lokacin da ya yi magana da manema labarai.

“Ina cikin ‘yan majalisa ta tara mai-ci, don haka ba zan sabawa abin da abokan aiki na su ka hadu a kai ba.” Sanata Ibrahim Gobir ya ke fadawa ‘yan jarida.

“Idan da shugabannin sojojin su na aiki da kyau, to babu dalilin a bukaci a tsige su. Duba abin da ya faru da gwamnan jihar Borno a kan hanyarsa ta zuwa Baga, abin kunya ne ga jami’an tsaronmu, shiyasa akwai bukatar a canza hafsun tsaro domin mu cigaba.”

‘Dan majalisa ya yi tir da ta’adin da miyagun ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane su ke yi a yankin Arewa maso yamma da a baya ya ke cikin zaman lafiya.

KU KARANTA: Gwamnan Katsina ya gana da Buhari a kan lamarin tsaro

Ibrahim Gobir ya hakikance a kan sauya Hafsun Sojoji saboda matsalar tsaro
Majalisar Dattawa Hoto: Senate/Twitter
Asali: UGC

“Ba mu taba mafarkin wannan musiba da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da su ka jefa mu ba.”

Duk da Gobir ya yabawa kokarin da sojojin Najeriya su ka yi na kawo zaman lafiya a yankinsa na gabashin jihar Sokoto, ya yi kira ga jami’an tsaron su kara kokari.

Kun san cewa ba su yi kokari ba a baya, amma yanzu da na ke magana, sojojin da aka tura zuwa yankina su na bakin kokarinsu, yanzu ba mu jin labarin satar mutane.”

“Mu na fama da matsalar tattali, amma tsaro babban nauyi ne a kan kowane gwamnati, babu kudin da za a kashe kan kare rai da za a ce ya yi yawa.” Inji Sanatan.

Sanata Muhammad Ali Ndume a gefe guda kuma ba ya goyon bayan a sauya hafsun tsaron kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng