Hari kan tawagar gwamna: Hedikwatar tsaro ta mayar wa da Zulum martani
Kwanaki shidda bayan an kai hari kan tawagar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta ce babu hannun dakarun soji a harin da aka kai wa tawagar gwamnan.
A cikin makon jiya ne wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari kan tawagar gwamna Zulum yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Baga a karamar hukumar Kukawa.
Jim kadan bayan kai ma sa harin, gwamna Zulum ya nufi sansanin sojoji a fusace tare da dora alhakin harin da aka kai ma sa a kan dakarun soji.
Gwamna Zulum ya zargi dakarun soji da yin kafar ungulu ga kokarin gwamnati na son kawo karshen hare - haren mayakan Boko Haram a jihar Borno.
Da ya ke magana yayin wani shiri na gidan Talabijin din Channels a ranar Laraba, kakakin hedikwatar rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya wanke rundunr soji daga aikata wani laifi.
Janar Enenche ya ce saboda nauyin zargin da gwamna Zulum ya yi, sai da hedikwatar rundunar tsaro ta gudanar da bincike kuma ta gano cewa babu gaskiya a cikin zargin.
"Nan da nan mu ka gudanar da bincike kuma mu ka gano cewa babu gaskiya a zargin da ake yi wa rundunar soji.
"Mun yi nazari a kan faifan bidiyon, hatta karar harbin bindigu da aka ji, ba irin na bindigun da rundunar sojin Najeriya ke amfani dasu ba ne.
DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya mayarwa da sarakunan kudancin Kaduna martani a kan zargin kwace kasa
"Daga sanin halayya da dabi'un mayakan Boko Haram da sojoji su ka yi, rundunar tsaro ta san cewa su ne su ka kai harin.
"Aikine na makiya, kamar yadda bincikenmu ya gano cewa makiyan kasa da ke yankin ne suka kai harin," a cewarsa.
Da ya ke kara jaddada cewa babu hannun rundunar soji a harin da aka kaiwa gwamna Zulum, Enenche ya ce masu ruwa da tsaki zasu karasa magana a kan lamarin.
Kazalika, ya kara da cewa rundunar tsaro ta kasa a shirye ta ke domin kawo karshen dukkan wasu kalubalen tsaro a fadin Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng