Ba mu daukan tubabbun ƴan Boko Haram aikin soja – Fadar gwamnati

Ba mu daukan tubabbun ƴan Boko Haram aikin soja – Fadar gwamnati

Fadar shugaban kasa a ranar Laraba ta karyata jita jitar da ake yada wa na cewa an dauki wasu daga cikin tubabbun yan Boko Haram aiki a Rundunar Sojojin Najeriya.

Wannan jita jitar ya bazu sosai a dandalin sada zumunta hara ta kai ga wasu 'yan Najeriya da dama sun fara shakku a kan shirin gwamnatin tarayya na sauya halin tubabbun yan taadan.

Jita jitar ta kara karfi jim kadan bayan Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya ce sojoji ne suka kai wa tawagarsa hari ba yan Boko Haram ba.

Ba mu daukan tubabbun ƴan Boko Haram aikin soja – Fadar gwamnati
Ba mu daukan tubabbun ƴan Boko Haram aikin soja – Fadar gwamnati
Asali: Twitter

Wasu yan Najeriya da dama a dandalin sada zumunta sun yi hasashen cewa akwai yiwuwar tubabbun yan Boko Haram da ake ikirarin an dauka aikin soja ne suka kai wa Zulum hari.

Sai dai cikin sanarwar ta ya fitar a ranar Laraba, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya ce wannan jita jitar ba gaskiya bane.

DUBA WANNAN: Dalilai 4 da yasa Shoprite za ta janye daga Najeriya

"Yana da muhimmanci mutane su san cewa babu wani tubabban dan Boko Haram da ya shiga aikin soja a Najeriya cikin wadanda aka yaye a shirin sauya musu mummunar akidarsu kuma ba a shirin daukansu aikin sojan a nan gaba," in ji shi.

Shehu ya yi karin haske game da shirin karbar tuban yan taadan da suka mika wuya suka ajiye makamansu kuma suka shiga shirin na sauya hali da koyar da su sanaa.

Ya ce Majalisar Dinkin Duniya, UN, da Tarayyar Kasashen Turai, EU da Kungiyar Yin Hijira ta Kasa da Kasa suna goyon bayan shirin.

Ba a daukan, "rikakkun yan ta'adda masu tsatsauran raayi a shirin na sauya halayen," a cewar Shehu.

Ya kara da cewa ana gudanar da bincike da tantancewa kafin a dauki tubabbun mayakan inda ya ce, "galibi wadanda aka tilasta musu shiga kungiyar ne ake dauka idan sun tuba da makamantansu ...".

Ya ce ana sa ran bayan an yaye su ba za su zama hatsari ga al' umma ba kuma domin an cusa musu kishin kasa da kyawawan halaye.

Shehu ya kara da cewa yana daga cikin hakkin alumma su karbe su muddin an tabbatar sun tuba. Idan dai ba sun sake daukan makamai ba ya kamata shugabannin alumma su hada kai da hukumomin da suka dace domin tabbatar da cewa an dena kyamar su.

Har wa yau, ya ce gwamnatin Buhari mai nagarta ce kuma tana laakari da halin da mutane ke ciki har da wadanda fitinar ta'adancin ya shafa da wadanda suka rasa yan uwansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel