Dalilin tsige mataimaki na – Kakakin Majalisar Edo, Okiye

Dalilin tsige mataimaki na – Kakakin Majalisar Edo, Okiye

Kakakin majalisar jihar Edo, Frank Okiye, ya ce an tsige mataimakinsa, Yekini Idiaye ne a ranar Laraba saboda wai ya hada baki da shugabannin jam'iyyar APC da gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ya kwace ikon majalisar 'da karfi da yaji'.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa an tsige Idiaye yayin zaman majalisar kuma aka maye gurbinsa da mamba mai wakiltar mazabar Orhionmwon II, Rolanda Asoro.

Kakakin majalisar, a jawabin da ya wallafa ta dandalin sada zumunta bayan tsige Idiaye, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya ja kunnen yayan jam'iyyarsa.

Dalilin tsige mataimaki na – Kakakin Majalisar Edo, Okiye
Dalilin tsige mataimaki na – Kakakin Majalisar Edo. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

Ya yi wa jawabin lakabi da "Bukatar da ke da akwai na jan kunnen gwamnan Imo da Shugabannin APC na jihar Edo a kan shirinsu na kwace iko a Majalisar Jihar Edo ta hanyar tashin hankali da rashin bin doka."

DUBA WANNAN: Yaki da COVID-19: Ganduje ya zama gwarzo a tsakanin gwamonin Najeriya

Ga wani sashi cikin jawabin Okiye , "Mun samu daga sahihiyar majiya cewa gwamnan Imo, Hope Uzodinma da masu ruwa da tsaki a APC a jihar Edo suna shirin kawo sandan ikon majalisa na bogi domin kwace iko a majalisar jihar Edo da hadin bakin tsohon mataimakin kakakin majalisa da ya nuna goyon bayansa ga dan takarar APC a baya bayan nan."

"Saboda haka muna kira ga Shugaban Tarayyar Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari da fadar shugaban kasa ta ja kunnen gwamnonin ta da wadanda suke aiki tare da shi don aiwatar da wannan barnar su kuma rika bin dokokin jiha.

"Jihar ta riga ta dau zafi saboda shirin zabe da yakin neman zabe da ake gudanarwa. Abinda suka yi niyyar aikatawa ya yi dai dai da ingiza rikici a yanayin da dama saura kiris rikin ya barke.

"Muna kira ga mutanen Edo, wadanda yan majalisa ke wakilta su tashi su nuna rashin amincewarsu ga irin wannan rashin bin dokar da amfani da baki domin dagula musu lissafi.

"Muna kira ga masoya demokradiyya a dukkan duniya da hukumomin dabbaka demokradiyya suyi tir da wannan shirin na yunkurin na kokarin hambarar da zababbun yan majalisa da saba doka."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164