‘Yan Kungiyar Boko Haram sun fito da sabon bidiyon sallar idi a Jihar Neja
Rahotanni na yawo cewa wasu dinbin ‘tan ta’addan kungiyar Boko Haram na bangaren Abubakar Shekau, sun fitar da sabon bidiyo na musamman.
‘Yan ta’addan da su ka yi wa Abubakar Shekau mubaya'a sun ce sun dauki wannan bidiyo ne a jihar Neja da ke a yankin Arewa maso tsakiyar kasar.
Malam Audu Bulama Bukarti, wani masanin harkar tsaro ya bayyana wannan a shafinsa na Twitter dazu.
A wannan bidiyo an ga mutane kimanin dari su na gabatar da sallar idi a kungurmin daji. Daga baya wasu sojoji uku su ka yi jawabin barka da sallah.
Wadannan mayaka sun yi magana ne da harshen Hausa, Ingilishi da kuma Fulfulde.
Bukarti wanda yanzu haka ya ke tare da cibiyar Tony Blair da ke Landan, ya ce idan har ta tabbata ‘Yan ta’addan sun ratsa jihar Neja, Najeriya ta na fuskantar barazana.
KU KARANTA: Boko Haram sun kashe mutane a IDP a kasar Kamaru
Masanin ya ke cewa Boko Haram za su iya kai hari a babban birnin tarayya da kuma kewayen Kwara da Kogi muddin su ka isa Neja da ke tsakiyar kasar.
Wani soja ya ke cewa a bidiyon: “Mu ne Jama’atu Ahlil Sunnah lil Dawatul Jihad a yankin Jihar Neja. Mu na so mu mika sakon gaisuwa, na farko ga Limaminmu, Abu Muhammad Ibn Muhammad Abubakar Shekau.”
Kamar yadda Bukarti ya lura, mayakan na Boko Haram su na dauke ne da kayan sojoji da ‘yan sanda, hakan ya nuna ‘yan ta’addan sun aukawa jami’an tsaron kasar.
A cewar Bukarti, a tsohon bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar a jihar Neja, wanda ya yi magana ya na sanye ne da kayan mutanen gari ba khakin jami’an tsaro ba.
A daidai lokacin da gwamnati ta ke cewa za ta yi wa harkar tsaro garambawul, ana cigaba da kira ta kare al’umma.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng