Hukumar PPPRA ta tsaida kudin litar mai a manyan tashoshi a kan N138.62

Hukumar PPPRA ta tsaida kudin litar mai a manyan tashoshi a kan N138.62

- Gwamnati ta yi karin N6 a kan farashin da aka saba sayen man fetur

- Litar fetur za ta rika tashi a tashoshi a kan kusan N139 a watan nan

- Wannan zai sa masu sayen fetur a gidajen mai su ga canji nan gaba

A ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2020, hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan mai a Najeriya ta yi karin Naira shida a kan litar man fetur.

PPPRA ta maida kudin litar man fetur N138.62 a manyan tashoshin kasar. Wannan shi ne kudin da za a saida mai kafin ayi jigilarsa zuwa gidaje a watan Agusta.

Dama can kun ji ‘yan kasuwan kasar su na kokarin ganin an maida kudin litar fetur tsakanin N149 zuwa N150 a dalilin wannan canji farashi da aka samu a tashoshi.

A farkon makon nan ne wani ‘dan kasuwa ya shaidawa jaridar Punch cewa kudin fetur zai iya komawa N150 a gidajen mai a wannan watan da aka shiga.

Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN ta manyan masu saida mai a kasa, Abubakar Maigandi, ya ce har yanzu PPPRA ba ta sanar da su sabon farashin da aka sa ba.

KU KARANTA: A kara kudin man fetur - PPPRA

Hukumar PPPRA ta tsaida kudin litar mai a manyan tashoshi a kan N138.62
Motar mai a Najeriya
Asali: Facebook

“Sun fada mana yau (Talata) cewa kudin lita a tasha ya zama N138.62, amma sun yi shiru game da farashin da za a saida fetur a fanfon gidan mai.” Inji Abubakar Maigandi.

Maigandi ya kara, “Da wannan kari na N6 a kan kowane lita, hasashenmu shi ne farashin gidan mai zai fado tsakanin N149 ko N150."

Da aka nemi aji ta bakin mai magana da yawun bakin PPPRA, Kimchi Apollo, bai amsa kiran waya ba. Kafin nan ya ce hukumar ba ta fitar da matsaya ba.

Wannan mataki da gwamnati ta dauka ya sa masu gidajen mai su na ta sayen fetur su na boyewa, yayin da ake jiran hukuma ta fito ta bayyana sabon farashi.

Watanni kusan shida kenan a Najeriya, ana saida mai ne a kan yadda farashi ya kaya a kasuwar Duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel