Sabanin NIPOST v FIRS, Ali v Adeosun, Pantami v Dabiri, Malami v Magu

Sabanin NIPOST v FIRS, Ali v Adeosun, Pantami v Dabiri, Malami v Magu

A ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2020, mutanen Najeriya su ka wayi gari da labari maras dadi na musayar kalamai tsakanin hukumomin NIPOST da FIRS na kasa.

Hukumar NIPOST ta samu sabani da FIRS mai alhakin tara haraji ne game da batun saida hatimin gwamnati, wannan sabani ya kai ana yi wa juna raddi a shafin Twitter.

Ba wannan ba ne karon farko da rashin fahimta ya shiga tsakanin jami'an ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.

Legit.ng Hausa ta kawo wasu daga cikin irin wadannan sabani:

1. Dr. Isa Ali Pantami v Farfesa Umar Garba Danbatta

Kwanakin baya an samu sabani tsakanin Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami da Umar Garba Danbatta wanda har ta kai Ministan ya hana shugaban NCC gabatar da wani jawabi a gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari.

2. Dr. Isa Ali Pantami v Abike Dabiri-Erewa

Haka zalika a kwanan nan, takaddama ta barke tsakanin Isa Ali Pantami da shugabar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, inda jami’an gwamnatin su ka fito su na maidawa juna martani a Twitter.

3. Ibe Kachikwu v Maikanti Baru

Tsohon ministan mai, Dr. Ibe Kachikwu ya taba aikawa shugaban kasa takarda ya na zargin tsohon shugaban kamfanin NNPC na kasa, Marigayi Dr. Maikanti Baru da rashin bin ka’idar aiki.

4. Abubakar Malami v Ibrahim Magu

Sabanin da ke tsakanin ministan shari’a Abubakar Malami (SAN) da Ibrahim Magu ya fito fili har aka dakatar da mukaddashin na hukumar EFCC daga bakin aiki, aka kuma fara bincikensa.

KU KARANTA: Buhari, Osinbajo su na ganawa da Hafsun Sojoji

Sabanin NIPOST v FIRS, Ali v Adeosun, Pantami v Dabiri, Malami v Magu
Shugaban Najeriya Buhari
Asali: UGC

5. Ibrahim Magu v DSS

Ibrahim Magu wanda ya hau kujerar shugaban EFCC a 2015 ya gamu da barazana daga hukumar DSS. Hukumar ta na zarginsa da ba daidai ba, kuma ta bada shawarar a hana shi rike EFCC.

6. Hameed Ali v Kemi Adeosun

An kuma samu sabani tsakanin shugaban hukumar kwastam na kasa, Hameed Ibrahim Ali da tsohuwar ministar kudi, Kemi Adeosun a game da kudin shigar da hukumar ta ke tatsowa.

7. Saleh Mamman v NBET da TCN

Wani rikici da aka yi kwanan nan shi ne tsakanin ministan wuta, Saleh Mamman da shugabar NBET, Marylin Amobi da kuma shugaban TCN. Wadannan sabani sun jawo abin magana tsakanin Mamman da Ministar kudi, Sakataren gwamnati da ma wasu kungiyoyin kwadago.

8. NHIS v Ministan lafiya

A 2017, an yi ta samun matsaloli tsakanin shugaban hukumar FIRS na kasa, Farfesa Usman Yusuf da kuma Ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole. Wannan ya yi sanadiyyar korar Yusuf daga aiki.

9. IGP: Ibrahim K. Idris v Solomon Arase

Shekaru hudu da su ka wuce aka rika cacar baki tsakanin tsohon IGP Solomon Arase da Ibrahim K. Idris bayan ya zama Sufetan ‘Yan Sanda a kan zargin tserewa da wasu motocin 'yan sanda.

An kuma yi ta samun irin wannan matsala tsakanin Aisha Muhammadu Buhari da jami’an gwamnatin mai gidanta irinsu Marigayi Abba Kyari, Garba Shehu da kuma wasunsu.

10. Ladan Salihu v Festus Keyamo

A ‘yan kwanakin bayan nan an samu matsala tsakanin Darekta Janar na hukumar samar da ayyuka na kasa da kuma karamin kwadago, Festus Keyamo a game da daukan ma’aikata 774, 000.

11. Chris Ngige v NSITF

Haka zalika babban Ministan kwadago na kasa, Dr. Chris Ngige ya samu matsala da shugabannin da ke lura da ma’aikatar NSITF, ya zargi ma’aikatar da batar da Naira biliyan 48.

12. Godswill Akpabio v John Nunieh

Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio da John Nunieh ta ma’aikatar Neja-Delta sun samu sabani, a karshe dole Nunieh ta bar ofis, ta rika jifan Ministan da zargin sabawa dokar aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel