Wasika mai ratsa zuciya da Buhari ya aike wa Iyalan Isma'ila Funtua
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wa iyalan marigayi Malam Isma'ila Isa Funtua wasika
- Buhari ya aika wasikar ne wacce yasa hannu da kansa
- A wasikar da shugaban kasar ya rubuta da harshen Hausa, ya bayyana rasuwar Funtua a matsayin babban rashi ga kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wa iyalan marigayin marubuci kuma dan kasuwa, Malam Isma'ila Isa Funtua wasika wacce yasa hannu da kansa.
A wasikar da shugaban kasar ya rubuta da harshen Hausa, ya bayyana rasuwar Funtua a matsayin babban rashi ga kasar nan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kasar ya sanar da matar mamacin, Hajiya Hauwa, 'ya'yansa da kuma daukacin 'yan uwansa cewa rashin ba nasu bane su kadai, na daukacin jama'ar Najeriya ne.

Asali: UGC
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce: "Malam Isma'ila ya taimaka min tare da mulkina. Ya taimaka ta hanyoyi da yawa wurin karfafa gwamnati da Najeriya kafin rasuwarsa."
Ya kara da cewa, "a siyasa, Malam Isma'ila ya yi minista kuma dan kasuwa ne sannan dan kwangila wanda ya yi gine-gine da dama a Abuja."
Shugaban Buhari ya ce, "shine daraktan masakar Funtua na shekaru 30 kuma ya shugabanci masakar Zamfara.
"Malam Isma'ila ya taka rawar gani a fannin jaridanci don ya zama mamba a tsangayar 'yan jaridar ta duniya, IPI."
Kamar yadda shugaban kasar ya sanar a wata takarda da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, ya ce, "Yan Najeriya kowanne iri kuwa basu da wata magana a kansa da ta wuce alheri."
KU KARANTA KUMA: Abinda yasa Atiku, Saraki da Kwankwaso ba za su koma APC ba
Ya ce, "A dukkan rayuwar Isma'ila, an san shi da saukin kai, karamci da kuma kyautatawa jama'a."
Daga bisani, shugaban kasar ya yi kira ga wadanda Malam Isma'ila ya rasu ya bari da kada su bar shaidan ya shiga tsakaninsu don rarrabe kawunansu, ya yi fatan Allah ya yafe masa kuma ya saka shi a Aljanna.
Idan za ku tuna a ranar 20 ga watan Yuli ne, Mallam Isa Funtua, fada tarkon mai yankan kauna.
Marigayi Isa wanda tsohon minista ne a jamhuriya ta biyu, ya yi gamo da ajali ne a sakamakon bugun zuciya kamar yadda iyalansa suka bayyana.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng