Labari da dumi: NNPC ta sake yin wani gagarumin rashi

Labari da dumi: NNPC ta sake yin wani gagarumin rashi

- Allah ya yi wa Dr Joseph Thlama Dawha, tsohon manajan daraktan kamfanin NNPC rasuwa

- Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ce ta sanar da batun mutuwar nasa a ranar Litinin

- Dr. Dawha ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ta sanar da rasuwar tsohon manajan daraktanta, Dr Joseph Thlama Dawha.

Dr. Dawha ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, manajan bangaren hulda da jama'a, Dr. Jennie Obateru ya sanar a wata takarda a ranar Litinin da dare.

Manajan daraktan kamfanin, Malam Mele Kyari, ya nuna matukar damuwarsa a kan mutuwar farat daya da Dr. Dawha yayi, wanda shine manajan darakta na 16 na kamfanin.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yiwa babban Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass rasuwa, Buhari ya aika sakon ta'aziyya

Labari da dumi: NNPC ta sake yin wani gagarumin rashi
Labari da dumi: NNPC ta sake yin wani gagarumin rashi Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Malam Kyari ya ce daukacin NNPC ta na jimami tare da ta'aziyyar mutuwar tsohon GMD Dawha.

KU KARANTA KUMA: Ku sadu da Attajirin Najeriya da zai mallaki kamfanin Shoprite

Ya tabbatar da cewa ya taimaka wurin shugabanci tare da bada gudumawa a bangarorin ci gaba da kamfanin.

Ya bayyana mutuwar Dr. Dawha a matsayin babban rashi ga NNPC tare da Najeriya baki daya.

Dawha ne GMD na kamfanin tsakanin watan Augustan 2014 zuwa watan Augustan 2015.

A wani labari na daban, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wa iyalan marigayin marubuci kuma dan kasuwa, Malam Isma'ila Isa Funtua wasika wacce yasa hannu da kansa.

A wasikar da shugaban kasar ya rubuta da harshen Hausa, ya bayyana rasuwar Funtua a matsayin babban rashi ga kasar nan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasar ya sanar da matar mamacin, Hajiya Hauwa, 'ya'yansa da kuma daukacin 'yan uwansa cewa rashin ba nasu bane su kadai, na daukacin jama'ar Najeriya ne.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce: "Malam Isma'ila ya taimaka min tare da mulkina. Ya taimaka ta hanyoyi da yawa wurin karfafa gwamnati da Najeriya kafin rasuwarsa."

Ya kara da cewa, "a siyasa, Malam Isma'ila ya yi minista kuma dan kasuwa ne sannan dan kwangila wanda ya yi gine-gine da dama a Abuja."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel