Hukumar NRC ta yi asarar N1bn saboda dakatar da harkoki

Hukumar NRC ta yi asarar N1bn saboda dakatar da harkoki

Hukumar jirgin kasa na Najeriya ta rasa kudaden shiga har sama da naira biliyan daya tsakanin watan Maris da Agustan wannan shekarar.

Hakan ya biyo bayan dakatar da harkokin jirgin kasa mai safarar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna ,da kuma Lagas zuwa Ijoko/Kajola da kuma jiragen kasa masu jigilar kayayyaki zuwa wurare mai nisa daga Lagas zuwa Kano.

Koda dai na Abuja zuwa Kaduna sun fara aiki a ranar Laraba sannan an kara kudin da kusan sama da kaso 100%.

Binciken jaridar Leadership ya nuna cewa jirgin Abuja zuwa Kaduna na samar da naira 6,890,000 a kullun da yawan fasinjoji 4,000, inda masu karamin karfi ke biyan akalla 1,300.

Gaba daya tana tara kimanin naira miliyan 50 duk sati da kuma naira miliyan 200 duk wata daga jigilar da take yi daga Abuja zuwa Kaduna.

Hukumar NRC ta yi asarar N1bn saboda dakatar da harkoki
Hukumar NRC ta yi asarar N1bn saboda dakatar da harkoki Hoto: Leadership
Asali: UGC

Baya ga tafiye-tafiye biyar da ake yi a kullun, hukumar kan yi jigila sau hudu a ranakun Laraba da fasinjoji 2,650, wanda ke daidai da samun N3,445,000 kan N1,300 kowani fasinja.

Wannan baya ga adadin fasinjoji masu shiga sahun yan kasuwa a jirgin Abuja zuwa Kaduna wanda ba za a iya kiyasta yawansu ba.

A Lagas, jirgin da ke jigila daga Iddo zuwa Ijoko/Kajola, ana karban N230 kan kowani tafiya.

Kowani tafiya na da kimanin tarago 10 zuwa 11 kuma akwai fasinjoji 90 da ke zama a kowani tarago da kuma sama da 200 da ke tsayuwa.

Ana jigila sau goma duk sati daga Litinin zuwa Juma’a sannan babu wanda ke tashi a Asabar da Lahadi.

Har ila yau bincike ya nuna cewa jirgin na daukar kimanin fasinjoji 11,000 duk sati sannan kowani fasinja na biyan N230 daga Ijoko da Kajola zuwa Iddo da Apapa.

An tattaro cewa baya ga jigilar tan 150 na kayayyaki duk shekara, jirgin Lagas na samar da sama da naira miliyan 50 duk wata.

Baya ga haka, hukumar NRC na gudanar da aiki a Port Harcourt zuwa Aba da kuma Lagas zuwa Kano a duk mako, wanda a cewar majiyoyi ya kan kasance cike.

Jirgin Warri-Itakpe na bunkasa sosai amma tun bayan da aka tsayar da ayyukan jiragen kasar sakamakon dokar kulle, abun ya shafi harkoki da tattalin arziki sosai.

KU KARANTA KUMA: Kamfanin Shoprite ya bada sanarwar zai daina kasuwanci a Najeriya

A cewar kungiyar ma’aikatan jiragen kasa (NURW), hukumar jirgin kasar na cin moriyar karin, musamman a jirgin Abuja zuwa Kaduna wanda ke daukar sama da fasinjoji 4000 a kullun.

Babban sakataren kungiyar, Kwamrad Segun Esan ya bayyana cewa a gaba daya hukumar na daukar fasinjoji sama da miliyan uku da kayayyaki sama da tan 150,000 duk shekara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel