Sanata Ndume ya goyi bayan samun shugaban kasa daga kudu a 2023

Sanata Ndume ya goyi bayan samun shugaban kasa daga kudu a 2023

- Sanatan Borno, Ali Ndume, ya ce jam’iyyar APC ba za ta marawa dan Arewa baya ya zama shugaban kasa a 2023 ba

- Dan majalisar ya yarda cewa idan har za a yi adalci da nuna daidaito, toh ya zama dole dan kudu ya zama shugaban kasa a 2023

- Ndume ya bayyana cewa sake barin dan arewa daidai yake da mika mulki ga shugaba Buhari a karo na uku

Fafutukar da ake yi na son mika shugabancin kasar ga dan kudancin Naeriya ya samu babban karbuwa bayan da Mohammed Ali Ndume, sanata mai wakiltan Borno ta kudu ya nuna goyon bayansa ga wannan kira.

Ndume ya bayyana matsayinsa a yayin wata hira da jaridar Nigerian Tribune wanda aka wallafa a ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta.

A cewar Ndume, zai zama daidai da adalci ne idan aka bari kudu ta karbi shugabancin kasar bayan cikar wa’adin shugaba mai ci a yanzu, Muhammadu Buhari a 2023.

Sanata Ndume ya goyi bayan samun shugaban kasa daga kudu a 2023
Sanata Ndume ya goyi bayan samun shugaban kasa daga kudu a 2023 Hoto: Daily Post
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban PDP na kasa ya sauya sheka zuwa APC

Ya ce: “Ta bangaren APC, tana so Shugaban kasa ya fito daga yankin Kudu kuma ina sahun gaba a wannan kiran saboda na yarda da daidaito da adalci kuma a duk inda babu daidaito da adalci, ba za a taba samun zaman lafiya ba.”

Ndume ya ci gaba da bayanin cewa a yayin kafa jam’iyya mai mulki, an mika shugabancin kasa ga arewa kuma zai zama adalci ne idan aka mikawa kudu a nan gaba.

“A lokacin da aka kafa APC, mun mika shugabancin kasa ga arewa. Shiyasa ‘yan takara hudu daga arewa da dan takara daya daga kudu maso gabas suka yi takara.

"Babu wanda ya yi takara daga kudu maso kudu da kudu maso yamma. Dan takara guda daya kawai ne Rochas Okorocha kuma kowa ya sani a wannan lokacin ya dai so ya dandani zumar yanci ne,” in ji shi.

Sanatan ya kara bayyana cewa ko jam’iyyar APC ba za ta goyi bayan Shugaban kasa daga arewa ba.

Barin dan takara dan arewa, ya ce daidai yake da mika ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari mulki a karo na uku.

“An ce dole a samu daidaito a mukamai, harma da nade-nade. An san matsayina a kan haka. Ba zan marawa dan takara daga arewa baya ba kuma bana tunanin APC za ta goyi bayan dan takara daga arewa. Dan takara daga kudu ne mafita.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel