Ba zan iya tuna adadin mutanen da na kashe ba - Tsohon ɗan Boko Haram

Ba zan iya tuna adadin mutanen da na kashe ba - Tsohon ɗan Boko Haram

Abdulwahab Usman, daya daga cikin tubabbun 'yan Boko Haram ya ce bai taba tsamanin zai samu samu irin kulawar da aka masa ba daga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Usman, wanda dan asalin garin Bama ne daga jihar Borno yana daya daga cikin tubabbun yan Boko Haram da suka kammala shirin sauya tunani da halayya na DRR a watan Yuli.

A shekarar 2016 ne Rundunar Sojojin Najeriya ta kaddamar da shirin na musamman na Operation Safe Corridor domin sauya wa tubbabun yan ta'adda tunani kafin mayar da su cikin al'umma.

A cewar jaridar Punch, Usman ya ce shi ba zai iya tuna adadin mutanen da ya kashe ba saboda yawansu amma duk da hakan gwamnati ta yi masa afuwa bayan ya mika wuya.

Ba zan iya tuna adadin mutanen da na kashe ba - Tsohon dan Boko Haram
Ba zan iya tuna adadin mutanen da na kashe ba - Tsohon dan Boko Haram. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna da bidiyo: Yadda Buhari da iyalansa suka yi Sallar Idi a Abuja

"Babu wanda aka kashe a cikin mu yayin shirin na sauya mana tunani. Na ji dadin zama na a sansanin domin mafi yawancin mu ba muyi tsamanin gwamnatin Najeriya za ta kyautata mana haka ba. Sun kula da mu sosai," in ji shi.

"Sun koyar mu da mu sana'o'i da dama. An koya mana sana'o'i da dama a cikin sansanin kamar aski, walda, kafinta d.s. Amma ni na zabi aski. Idan na koma garin mu zan cigaba da aski. Ba zan koma Boko Haram ba.

"An bamu Kur'ani mai girma saboda mun tabbatar za mu zama yan kasa na gari. Ba zan koma Boko Haram ba duk wuya ko azaba saboda gwamnati ta kula da mu.

"An tilasta min shiga kungiyar kimanin shekaru biyar da suka shude. Ba zan iya tuna adadin mutanen da na kashe ba da na ke Boko Haram saboda suna da yawa. Boko Haram sun zo kauyen mu suna neman matasa kuma a lokacin ne aka tilasta wa ni da abokai na shiga kungiyar. Daga baya sun tsere sai sojoji suka kai mu barrakinsu da ke Giwa a Borno."

Tsohon dan taaddan kuma ya roki gwamnati ta bawa sauran mayakan kungiyar tabbacin cewa za ayi musu afuwa idan har za su miya wuya.

"Gwamnatin Najeriya ta rubuta takarda a hukumance na tabbatar musu da cewa ba za a kashe su ba idan sun mika wuya," in ji shi.

Ya kara da cewa shi da sauran takwarorinsa 602 sun mika wuya ne bayan sun gani a rubuce cewa za a amshe su a kai su sansanin gyaran hali idan suka tuba.

Mutane da dama dai suna nuna kin amincewarsu da shirin gwamnati na sakin tubabun yan taadan su koma cikin mutane.

Mazauna Borno da suka yi magana da The Cable sun ce gwamnatin ta cigaba da ajiye su a hannun ta.

Sanata Ali Ndume mai wakiltan Borno ta Kudu shima baya goyon bayan shirin sauya wa yan Boko Haram halaye inda ya ce yan ta'adda ba za su taba tuba ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel