Mamman Daura: "Da cancanta aka bi ba yanki ba, a 2015 da Buhari bai yi mulki ba"

Mamman Daura: "Da cancanta aka bi ba yanki ba, a 2015 da Buhari bai yi mulki ba"

Wasu daga cikin kungiyoyin da ke kare mutanen Kudu da Arewacin Najeriya sun yi wa Mamman Daura raddi a game da maganar da ya yi na cewa cancanta zai yi aiki a zaben 2023.

Punch ta samu labari cewa kungiyoyi irinsu Middle Belt Forum, Ohanaeze Ndigbo, Afenifere da South-South Elders’ Forum ta mutanen Arewa, Ibo, Yarbawa, Neja-Delta sun yi magana.

A hira da kungiyoyin su ka yi da jaridar a mabanbantan lokaci, sun nuna ba su goyon bayan kiran da Mamman Daura ya ke yi. Sai dai kungiyar ACF ta manyan Arewa ta ce dattijon ya yi gaskiya.

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Cif Nnia Nwodo, ya yi magana ta bakin hadiminsa, Emeka Attamah, ya na mai cewa akwai son rai a kalaman da ‘danuwan shugaban kasar ya yi.

Nnia Nwodo ya tunawa Mamman Daura cewa an fatattaki Goodluck Jonathan daga mulki a 2015 ne saboda mutanen yankin Arewa su na ganin cewa lokacinsu ne da za su yi mulkin kasar.

“Idan ana maganar cancanta da dacewa da mulki, Buhari ne ‘dan Najeriyar da ya fi kowa cancanta a lokacin da ya zama shugaban kasa?” Nnia Nwodo ya tambayi Malam Daura.

KU KARANTA: Iyakata da Buhari shawara - Mamman Daura

Daura: Da cancanta aka bi ba yanki ba, a 2015 da Buhari bai yi mulki ba – Afenifere
Malam Mamman Daura
Asali: Twitter

Ohanaeze ta ce ana wannan magana ne don kurum lokaci ya yi da mutanen Kudu za su karbi mulki. Asali ma wanene ke cewa wannan ‘dan takara ne ya fi cancanta? Inji kungiyar.

Ita kuwa kungiyar Afenifere ta bakin Kakakinta, Yinka Odumakin, cewa ta yi: ”Kamata ya yi ace shi (Daura) ya kawo wannan magana kafin 2015, idan ya na nufin alheri.”

A na sa bangare, shugaban manyan Kudu maso kudu, Anabs Sara-Igbe ya ce Daura bai isa ya tsara inda mulki zai koma a 2023 ba, kuma a dalilin kama-kama ne ma Buhari ya samu mulki.

Shugaban Middle Belt Forum, Dr. Birtus Porgu ya ce hirar da aka yi da Daura ya nuna cewa Arewa su na yunkurin cigaba da mulki ne bayan 2023, ya kuma zargi Buhari da fitita mutanen yankinsa.

Takwaransa, Emma Zopmal wanda shi ne shugaban wata kungiya ta matasan Arewacin Najeriya ya ce: “Mamman Daura ba su natsu da wani ‘Dan Kudu ya karbi mulki a 2023 ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel