Obaseki ya fara shirya jawabin mika mulki - APC

Obaseki ya fara shirya jawabin mika mulki - APC

Kwamitin kamfen na jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo, karkashin shugabancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya nuna kwarin guiwar cewa zai sauke nauyin da ke kansa a zaben ranar 19 ga watan Satumba.

A cikin kwanakin nan ne aka nada Gwamna Ganduje don jagorantar kwamitin yakin neman kujerar gwamnan jihar Edo na jam'iyyar APC.

Osagie Ize-Iyamu da wata kungiya mai zaman kanta sun yarda da cewa APC za ta yi nasara a zaben gwamnan jihar Edo tunda Ganduje ne ke jar ragamar.

A takardar da shugaban kungiyar, Kwamared Salifu Momodu yasa hannu, ya jinjinawa kokarin Gwamna Ganduje tun bayan da aka nada shi a matsayin shugaban kamfen din.

Obaseki ya fara shirya jawabin mika mulki - APC
Obaseki ya fara shirya jawabin mika mulki - APC Hoto: The Sun
Asali: UGC

Kungiyar ta shawarci Gwamna Obaseki da ya fara tsara jawabin mika mulki saboda kungiyar kamfen ta Ganduje na matukar kokari don ganin nasarar Osagie Ize-Iyamu a watan Satumba.

"A bangarenmu, muna shawartar Gwamna Obaseki da ya fara shirya jawabin mika mulki saboda siyasarsa ta zo karshe.

"Muna so Gwamna Obaseki ya gane cewa, dan takarar jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu ne zai yi nasara a zaben ranar 19 ga watan Satumba mai zuwa. Tuni APC ta shirya don ganin wannan mafarki ya zama gaske.

KU KARANTA KUMA: 'Ba mu yarda ba': APC da PDP sun mayarwa da Mamman Daura martani

"Ba zamu sassauta ba wurin tabbatar da nasarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC). Ta hannun kwamitin yakin neman zaben gwamna a jihar za mu cima nasara a zaben."

A gefe guda, mun ji cewa abubuwa na neman rikicewa Godwin Obaseki, yayinda manyan ma'aikata da abokan aikinsa suke fita daga gwamnatinsa ana sauran yan makonnin zabe.

Gwamnan ya fara fuskantar wannan kalubale ne tun bayan lokacin da ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress APC zuwa jam'iyyar People Democratic Party PDP.

Sakamakon fitarsa, wasu mabiyansa irin tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Kabiru Adjoto, sun bi sahunsa.

Amma dai ga dukkan alamu an gano cewa wadanda suka fita daga tafiyar gwamnan sun fi adadin wadanda suka bisa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng