Rikicin kudancin Kaduna: Rashin isassun ma'aikata ke mayar mana da aiki baya - Rundunar soji

Rikicin kudancin Kaduna: Rashin isassun ma'aikata ke mayar mana da aiki baya - Rundunar soji

- Kwamandan rundunar Operation Safe Haven a Kaduna, ya ce rundunar sojin Najeriya basu da isassun ma'aikata da za su iya yakar rikici a kudancin Kaduna

- Chukwuemeka Okonkwo ya ce hukumar sojin kasar na kokarin tsara yadda za ta inganta tsaro

- Kwamandan ya yi kira ga yankunan da ke kudancin Kaduna da su rungumi zaman lafiya

Chukwuemeka Okonkwo, kwamandan rundunar Operation Safe Haven a Kaduna, ya ce sojin Najeriya basu da isassun ma'aikata da za su iya yakar rikici a kudancin Kaduna.

A yayin zantawa da manema labarai bayan taro a kan tsaro wanda Gwamna El-Rufai ya shugabanta, Okonkwo ya ce hukumar sojin kasar na kokarin tsara yadda za ta inganta tsaro.

Kwamandan ya ce za a tura karin soji yankin don dakile duk wani rashin tsaro da ke kawo asarar rayuka da dukiyoyin a yankin.

Rikicin kudancin Kaduna: Rashin isassun ma'aikata ke mayar mana da aiki baya - Rundunar soji
Rikicin kudancin Kaduna: Rashin isassun ma'aikata ke mayar mana da aiki baya - Rundunar soji Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Abinda muke samu shine hare-hare a wasu garuruwa da hare-haren daukar fansa. Kuna da matasan katafawa, Fulani da kuma 'yan ta'adda na bangarorin biyu," Okonkwo yace.

"Kowanne lamari ya isa ya haddasa rikici a wannan yankin, ana ta fama da hargitsa, fashi da makami da kuma satar dabbobi a wannan yankin.

"Mun sake duba yanayin aikin mu. Za mu sake dagewa. Idan aka kai hari daya zuwa biyu, za mu hana faruwar na ukun. Idan kun san yankin da kyau, a warware suke kuma akwai nisan kilomita masu yawa a tsakaninsu da juna. Ababen hawa na shan wuya kafin su isa.

"Kuma bamu da isassun ma'aikata amma kuma wadanda muke da su sun mayar da hankali. Amma za a sake tura ma'aikatan don gujewa matsalar rashin yawan."

Kwamandan ya yi kira ga yankunan da ke kudancin Kaduna da su rungumi zaman lafiya.

KU KARANTA KUMA: Nasarawa: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5, sun banka wa wasu gidaje wuta

Ya kara da cewa za a samar musu da wuri mai kyau da za su hadu, su tattauna sannan su sasanta matsalolinsu ba tare da fada ba, jaridar The Cable ta ruwaito.

Tun farko, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce mulkinsa ya yi duk abinda ya dace a kundin tsarin mulki don kawo zaman lafiya a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel