‘Yan takarar APC sun kai karar Akeredolu; ‘Yan PDP sun yi watsi da Jegede

‘Yan takarar APC sun kai karar Akeredolu; ‘Yan PDP sun yi watsi da Jegede

Alamu sun nuna cewa samun nasarar Eyitayo Jegede a matsayin ‘dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Ondo bai yi wa wasu ‘yan takara dadi ba.

Jaridar Daily Trust ta ce samun tikitin da Eyitayo Jegede ya yi, ya keta jam’iyyar PDP. Jegede ya yi galaba ne a kan wasu ‘yan takara bakwai har da mataimakin gwamna.

Tsohon kwamishinan shari’an na Ondo ya karbi satifiket a matsayin wanda zai rikewa PDP tuta a zaben Ondo. Jegede ya karbi takardar shaidan nasara ne a sakatariyar jam’iyyar.

Da ake mikawa Mista Eyitayo Jegede satifiket, mutum guda ne rak cikin wadanda su ka nemi takara ya yi masa rakiya, wannan ba kowa ba ne face Godday Erewa.

Sauran abokan neman takarar Jegede ba su take masa baya zuwa Abuja ba. Wannan ya sa jaridar ta ke ganin cewa akwai alamun baraka ta shiga tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar adawar.

Haka zalika mafi yawan ‘yan majalisar NWC na jam’iyyar PDP ba su nan a lokacin da sakataren PDP na kasa, Sanata Ibrahim Tsauri ya ba ‘dan takarar satifiket

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun yaba da kamun ludayin Buhari

‘Yan takarar APC sun kai karar Akeredolu; ‘Yan PDP sun yi watsi da Jegede
Eyitayo Jegede da Rotimi Akeredolu
Asali: Depositphotos

Shi kansa shugaban PDP, Prince Uche Secondus bai halarci taron ba. Wani babba da aka gani a sakatariyar a lokacin shi ne mataimakin shugaban PDP na Kudu, Yomi Akinwonmi.

Jegede ya fito ne daga shiyyar Ondo tsakiya, sauran ‘yan takarar gaba daya sun fito ne daga kudancin jihar. Mutanen tsakiyar Ondo sun yi mulkin jihar tsakanin 2008 zuwa 2016.

A jam’iyyar APC mai mulki, wasu ‘yan takara sun ma kai karar gwamna Rotimi Akeredolu ne a gaban uwar jam’iyya kamar yadda jaridar ta bayyana a wani rahoton.

A ranar Litinin, 28 ga watan Yuli, Rotimi Akeredolu ya bayyana gaban babban kwamitin sauraron korafin zaben tsaida ‘dan takara da jam’iyyar APC ta shirya a makon jiya.

Akeredolu ya doke mutane 11 a zaben, amma wasu daga cikin ‘yan takarar su na kukan an sabawa doka a zaben da ya ba gwamnan nasara don haka su ka kai kuka gaban kwamiti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel