Nasarawa: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5, sun banka wa wasu gidaje wuta

Nasarawa: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5, sun banka wa wasu gidaje wuta

- 'Yan bindiga sun halaka mutum biyar a kauyen Dawusu da ke karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa

- Daga cikin wadanda aka kashe harda matar aure sannan suka kona wasu gidaje

- Sarkin kauyen, Alhaji Abdullahi Usman, ya tabbatar da aukuwar lamarin

Wasu mutane da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe mutum biyar da suka hada da matar aure a kauyen Dawusu da ke karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa.

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya mai suna Salihu, ya ce lamarin ya auku ne wurin karfe 10 na daren ranar Litinin yayin da mazauna kauyen ke bacci.

'Yan bindigar sun shiga kauyen tare da hargitsa yankin.

Ya ce wadanda ake zargin 'yan bindigar ne sun kashe mutum biyar da suka hada da matar aure tare da bankawa gidaje wuta.

Ya kara da cewa an ji 'yan bindigar na ihun Allahu Akbar yayin da suke raunata wasu mazauna yankin sannan kuma suka tsere ta rafin garin bayan kammala harin.

Nasarawa: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5, sun banka wa wasu gidaje wuta
Nasarawa: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5, sun banka wa wasu gidaje wuta Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sarkin kauyen, Alhaji Abdullahi Usman, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata tattaunawar waya da yayi da jaridar Daily Trust.

Ya ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu.

KU KARANTA KUMA: Ci gaba da barin hafsoshin tsaro a kan mukaminsu babbar musiba ce ga Najeriya - Junaid

Ya ce, "a takaice dai gawawwaki hudu aka kawo fadata da ranar nan kuma mun sallacesu. 'Yan sintiri da suka shiga daji sun gano gawa daya."

Basaraken, wanda ya nuna damuwarsa a kan hare-haren da ya addabesu ya ce, "A makon da ya gabata ne aka yi garkuwa da wasu mutum biyu a kan hanyarsu ta zuwa gona. Har yanzu ba a sako su ba."

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, ya ce ya yi kokarin tuntubar DPO na yankin don tabbatar da aukuwar lamarin amma bai yi nasara ba.

A wani labarin kuma, kungiyar matasan addinin Musulunci na kudancin Kaduna (MYFOSKA), sun yi zargin yawan kashe-kashen mambobinsu wadanda ke hanyar tafiya ko wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullun a kudancin Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yankunan kudancin Kaduna na fama da kashe-kashe daga ‘yan bindiga da kuma hare-haren ramuwar gayya tsakanin manoma da makiyaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel