Mike Ozekhome SAN ya hadu da kwamitin Ayo-Salami, ya fitar da hujjoji
A ranar Talata, 28 ga watan Yuli, shararren Lauyan nan, Mike Ozekhome ya hallara gaban kwamitin Ayo Salami, ya rantse tare da bada shaida a kan Ibrahim Magu da ake bincike.
Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa Mike Ozekhome SAN ya bada wasu hujjoji shida a kan tsohon mukaddashin shugaban na hukumar EFCC da aka dakatar.
Daga cikin hujjojin da wannan Lauya ya bada a kan Ibrahim Magu, har da wasu bidiyoyi da wasu takardu. Rahoton ya ce wannan ganawar ta su ta dauki kimanin sa’o’i biyu.
Lauyan ya yi wa kwamitin bayanin zargin da ake yi wa Magu na gazawar shugabanci a hukumar EFCC da kuma rashin iya binciken masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.
Mike Ozekhome ya bada shawarar cewa ya kamata hukumar EFCC ta kara sanin makamar aiki, ta kuma daina fitowa ta na bayyanawa ‘yan jarida lamarin shari’a kafin shiga kotu.
KU KARANTA: Yadda na yi da motocin da na karbe - Magu
Lauyan da ke kare tsohon mukadasshin shugaban na EFCC, Mista Tosin Ojaomo ya shaidawa manema labarai cewa ya san da zuwan Ozekhome SAN gaban kwamitin binciken.
Ojaomo ya koka da yadda kwamitin ya gayyaci Ozekhome amma ba a ba Magu damar ya kare kan shi ba. Lauyan ya ce kowa ya san yadda Ozekhome ya saba sukar Magu da hukumar EFCC.
Lauyan ya zargi kwamitin da kokarin kama Magu da rashin gaskiya ko ta wani irin hali, ya ce don haka ne kwamitin ya ke gayyatar masu jin haushin EFCC irinsu Magu Ozekhome.
Ozekhome ya shaidawa jaridar cewa an gayyace shi ne domin ya ba kwamitin shawarwari, ya ce ya kuma yi wannan, har ya gabatar da wata takarda da ya tabawa aikawa Yemi Osinbajo.
Babban lauyan ya ce burinsa shi ne yadda za a gyara kura-kuran da ake yi a EFCC, ba wai barje takun sakan da ke tsakaninsu ba, ya ce bai yi maganar kudinsa da Magu ya taba karbewa ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng