Ministoci za su amsa tambayoyi a Majalisa a kan aikin Abuja-Kaduna da aikin dogo

Ministoci za su amsa tambayoyi a Majalisa a kan aikin Abuja-Kaduna da aikin dogo

- Sanatoci sun aikawa Babatude Fashola, Zainab Ahmed, NISA da AGF takarda

- Ministocin za su yi bayani ne game da wasu ayyuka da NSIA ta ke yi a Najeriya

- Amaechi da Pantami za su bayyana a gaban ‘Yan Majalisar wakilai bayan hutu

A ranar Talata, majalisar dattawa ta aikawa Ministocin kudi da na ayyuka da gidaje, Hajiya Zainab Ahmed da Babatunde Fashola gayyatar cewa ta na so ta gansu.

‘Yan majalisar su na so su ji halin da ake ciki game da manyan ayyuka uku da gwamnatin tarayya ta ke yi. Daga cikin wadanda aka aikawa takarda har da AGF da shugaban ma’aikatar NSIA.

Ministocin, babban Akawun gwamnati, Ahmed Idris da Mista Uche Orji za su yi bayanin inda aka kwana a kan aikin titin Abuja zuwa Kano, da na Legas zuwa Ibadan da kuma gadar Neje-Delta.

Sanata Solomon Olamilekan ya ce an gayyaci jami’an gwamnatin zuwa gaban majalisa ne domin su yi karin bayani a kan banbance-banbance da aka samu a kudin wadannan kwagiloli.

KU KARANTA: Karya Minstan N/Delta ya yi kan batun kwangilolin NDDC – Sanatoci

Ministoci za su amsa tambayoyi a Majalisa a kan aikin Abuja-Kaduna da aikin dogo
Taron Majalisar Ministoci Hoto: Aso Villa
Asali: UGC

Gwamnatin kasar ta na yin wannan ayyuka ne ta karkashin tsarin PIDF wanda ma’aikatar NSIA ta ke lura da shi. Ma’aikatar ta ce ta fitar da Naira biliyan 230 ga ‘yan kwagilan da ke aikin.

Kafin yanzu Orji ya fadawa Sanatoci cewa da farko kwangilolin su na karkashin ma’aikatar ayyuka da gidaje ne kafin su dawo karkashinsa, don haka babu ruwansa da bashin da ya taru.

A daidai wannan lokaci kuma majalisar wakilai ta bukaci ganin Ministan sufuri, Rotimi Ameachi, tattalin arzikin zamani da sadarwa, Dr. Isa Ali Pantami da ministar kudi, Zainab Ahmed.

Majalisar wakilan ta na so ministocin su yi karin haske ne game da bashin Dala miliyan 500 da gwamnati za ta karba daga wani bankin kasar Sin domin ayyukan dogo a Najeriya.

Honarabul Ossai Nicholas Ossai ya ce daga cikin wadanda za su hallara da ministocin a ranar 17 ga watan Agusta, har da shugabar ma’aikatar da ke lura da bashin Najeriya, Patience Oniha.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng