‘Dan wasan gaban Real, Mariano Diaz ya kamu da kwayar COVID-19

‘Dan wasan gaban Real, Mariano Diaz ya kamu da kwayar COVID-19

- Real Madrid ta ce ta gano Mariano Diaz ya na dauke da Coronavirus

- ‘Dan wasan gaban ya na killace a gida domin gudun yada wannan annoba

- Watakila Tauraron ba zai buga wasan Real da Manchester City ba

Kungiyar Real Madrid ta bada sanarwar cewa ‘Dan wasan gabanta, Mariano Diaz, ya kamu da kwayar cutar COVID-19.

A yayin da annobar Coronavirus ta ke cigaba da barna a Duniya, ‘dan kwallon kasar Jamhuriyyar Dominican, Mariano Diaz ya shiga sahun masu dauke da cutar.

Mariano Diaz Mejia mai shekaru 26 a Duniya ya na bugawa Real Madrid ne a matsayin mai zura kwallo a raga.

Larurar da ta kama ‘dan wasan ya sa kungiyar ta na tunanin Diaz ba zai buga wasanta da za ta yi da Manchester City a Ingila a ranar 8 ga watan Agusta ba.

A ranar Litinin, 27 ga watan Yuli, 2020, Real Madrid ta yi wa Zakarunta na La-liga gwaji, an yi rashin dace ‘dan wasan gaban ne aka samu da cutar.

KU KARANTA: COVID-19 ta kama 'Dan kwallon Najeriya a Turai

‘Dan wasan gaban Real, Mariano Diaz ya kamu da kwayar COVID-19
Mariano Diaz Hoto: Real Madrid
Asali: Getty Images

Real Madrid ta fitar da gajeren jawabi ta na cewa: “Bayan gwajin COVID-19 da malaman kiwon lafiyar mu su ka yi wa kowane daga cikin manyan ‘yan wasanmu, sakamakon Mariano ya nuna ya na dauke da kwayar.”

“’Dan wasan ya na cikin koshin lafiya kuma ya na bin dokokin zaman kulle a gida.”

A mako mai zuwa ne Real Madrid za ta buga wasa mai zafi da Manchester City. A zagayen farko na wasan an doke Real a gida da ci 1-2.

Idan ‘dan wasan bai warke ba, zai yi wahala a iya tafiya da shi zuwa birnin Manchester domin buga wasan gasar zakarun Nahiyar Turai a watan gobe.

Kawo yanzu Diaz ne kadai ‘dan wasan Real Madrid da aka samu labarin ya kamu da COVID-19.

A Sifen mutane fiye da 320, 000 sun kamu da COVID-19, an kuma samu kusan mutum 30, 000 da cutar ta kashe daga farkon shekara zuwa yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng