An damke tsohuwa ‘yar shekara 60 da ake zargi da fashi da makami a Kano

An damke tsohuwa ‘yar shekara 60 da ake zargi da fashi da makami a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da wasu da ake zargi da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifukan ta’addanci a jihar da kewayenta.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa daga cikin wadanda ake zargi harda wata Misis Aisha Isyaku, ‘yar shekara 60.

Aisha ta kuma kasance uwa ga biyu daga cikin wadanda ake zargin masu suna Ibrahim Isyaku wanda aka fi sani da Kawu, da Ahmadu Isyaku wanda ake kira Shiddi.

An tattaro cewa Kawu mai shekaru 35 da Shiddi mai shekaru 45 sun far ma wani mai suna Abdullahi Isah, sannan suka yi masa fashin kudi naira 400,000.

Sun hadu da bacin rana ne lokacin da ‘yan sanda suka kama su a wani gida a kauyen Rantan, karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano.

An samo bindigogin AK-47 guda biyu, mujalla biyu dauke da alburusai41, bindiga guda da harsashi hudu, kayan sojoji da kuma rigar aiki guda daga wajen iyalan Isyakun.

An kuma kama mahaifiyarsu a lokacin da take kokarin boye rigar yakin masu laifin a cikin wata jaka.

An damke tsohuwa ‘yar shekara 60 da ake zargi da fashi da makami a Kano
An damke tsohuwa ‘yar shekara 60 da ake zargi da fashi da makami a Kano Hoto: The Nation
Source: UGC

Kamun nata ya yi sanadiyar kama wani dan shekara 40, Abdulkadir Musa wanda aka fi sani da Malam Malam, a kauyen Yan Mariya, karamar hukumar Tudun Wada da ke jihar. An samo wani ganga guda da harsashi daya daga wajen shi.

An kuma ragargaji wata tawaga da su Isyaku ke jagoranta, wadanda suka kai farmaki gidan Shugaban karamar hukumar Birniwa a kauyen Dolen-Kwana, jihar Jigawa inda suka kashe wani jami’in dan sanda, Sajen Mohammed Ibrahim, wanda ke kan aikin gadi.

KU KARANTA KUMA: PDP ta bayyana dalilin da yasa Dogara ya koma APC

An kuma gano bindigar marigayi dan sandan da aka sace a wajen Kawu wanda ya amsa laifinsa.

Kwamishinan yan sandan jihar, Habu Sani, ya bayyana bindigar yayinda ya gurfanar da wadanda ake zargin.

Har ila yau, tawagar Operation Puff-Adder sun yi nasarar kama Yahuza Ibrahim mai shekaru 40 da kuma Hassan Umar mai shekaru 24. An kwato mota kirar Honda Henessy.

An tattaro cewa Ibrahim da Umar sun yi garkuwa da Lawan Abdullahi mai shekaru 73 sannan suka nemi a biya fansa mai tsoka.

Bincike ya yi sanadiyar kama wani Musa Alhaji Lawan mai shekaru 37, wanda ya kasance dan aikin mutumin. An gano cewa sunan Lawan na gaskiya Abdulhadi Falalu.

Sani, wanda ya yi jawabi ga manema labarai, ya ce cikin mutum 392 da aka kama akwai masu fashi da makami 30, masu garkuwa da mutane 26 da kuma ‘yan daba 312.

Har ila yau an gurfanar da ‘yan damfara 11, masu fataucin miyagun kwayoyi 15 da barayin mota 14.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel