Obono-Obla: Yau Shugabannin Jam’iyyar APC kansu kawai su ka sani ba Talakawa ba

Obono-Obla: Yau Shugabannin Jam’iyyar APC kansu kawai su ka sani ba Talakawa ba

Tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa na bankado dukiyar gwamnati da ke hannun mutane, Okoi Obono-Obla ya yi hasashen watakila jam’iyyar ba za ta ci zaben 2023 ba.

Cif Okoi Obono-Obla ya ce shugabannin jam’iyyar APC sun sa son-rai a cikin al’amuransu, ya ce akwai abin damuwa game da yadda ake tafiyar da jam’iyyar mai mulki.

Obono-Obla ya ke cewa shekaru bakwai da kafa jam’iyyar APC a Najeriya, har yanzu babu rajistar da ke dauke da sunayen ainihin ‘ya ‘yan jam’iyyar.

A wani jawabi da ya yi a dandalin sada zumunta, tsohon hadimin shugaban kasar ya hango rugujewar APC idan har jam’iyyar ta gaza yin garambawul, ta yi gyara, ta sake shirya kanta.

A cewar Obono-Obla, idan har jam’iyyar ta APC ba ta yi hakan ba, za ta sha wahala wajen jawo hankalin ‘Yan Najeriya a babban zabe mai zuwa.

“APC ba ta yi dace da shugabannin kwarai ba tun lokacin da aka kafa ta. Wannan ya jawo nasarorin da jam’iyyar ta samu su ke yin kasa.”

KU KARANTA: Gwamnan Edo da Tawagarsa sun sha ihu gaban Sarki

Obono-Obla: Shugabannin Jam’iyyar APC kansu kawai su ka sani ba Talakawa ba
Okoi Obono-Obla
Asali: UGC

“Shugabannin jam’iyyar da ‘ya ‘yanta sun ginu ne a kan son-kai da raba mutane. Dole ta hadu, ta yi kokarin dinke duk wasu baraka da ke cikin jam’iyyar domin a dunkule a zama tsintsiya guda.”

A cewar masanin shari’ar, jam’iyyar ta na bata lokacinta a kan abubuwan da ba su kai sun kawo ba.

Jam’iyyar ta saki layi daga manufofi da akidun shugabanninta, ‘ya ‘yan ta sun koma neman hanyar da za su azurta kansu da na kusa da su a madadin talakawa inji Obla.

Ya ce: “Jam’iyyar yanzu ta zama gungun ‘yan son cin banza da handamammun da ke yunkurin cin zabe ko ta wani irin hali domin su samu kudi da kujerar gwamnati."

A 2019 ne shugaban kasa ta hannun sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sallami Obono-Obla daga aiki bisa zargin yin karya da wasa da kudin gwamnati.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel