Babu wanda ya isa ya murde zaben Gwamnan Jihar Edo – Gwamna Wike

Babu wanda ya isa ya murde zaben Gwamnan Jihar Edo – Gwamna Wike

Mai girma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike ya bayyana cewa daukacin yankin Kudu maso kudancin Najeriya shiyyar jam’iyyar PDP ce.

Mista Nyesom Ezenwo Wike ya yi wannan jawabi ne wajen kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP a zabe gwamnan jihar Edo a ranar Asabar.

A ranar 25 ga watan Yuli, 2020, jam’iyyar PDP ta bude yakin neman zabe a Edo ne a babban filin wasan Samuel Ogbemudia da ke garin Benin.

Channels TV ta rahoto Nyesom Wike wanda shi ne shugaban yakin neman zaben PDP a Edo ya na cewa siyasar uban-gida ta zo karshe a jihar Kudu maso kudun.

“Dole mutanen jihar Edo su ki yarda da siyasar uban-gida domin babu wanda zai iya murde zaben gwamnan ranar 19 ga watan Satumba a jihar nan.” Inji Wike.

Ya ce: “Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya yi amai ya lashe da tsaida ‘dan takarar da a baya ya yi fatali da shi kuma ya caccake shi.”

KU KARANTA: Abin da ya sa na koma APC - Dogara

Babu wanda ya isa ya murde zaben Gwamnan Jihar Edo – Gwamna Wike
Gwamna Wike da Atiku Abubakar Hoto: PDP
Asali: UGC

Wike ya cigaba da bayani, ya na cewa: “Yau mun zo ne mu fadawa mutanen Edo cewa ka da su ji tsoron kowa saboda babu wanda zai iya magudi a zaben da za ayi.”

“Yau ce karshen siyasar uban-gida a jihar Edo. Ina so in yabawa gwamna Godwin Obaseki da ya ki taka rawar uban gida.”

“Shekaru hudu da su ka wuce Adams Oshiomhole ya ce ba zai yarda da ‘dan takarar APC da aka kora daga makaranta ba. Yau Oshiomhole ya dawo ya gabatarwa mutanen Edo wannan mutumi.”

Gwamnan Ribas ya ce: “Ya dauka mutanen jihar Edo sakarkaru ne. Ina kalubalantar mutanen Edo ka da su zabi ‘dan takarar da Adams Oshiomhole ya kawo masu.”

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto ya yi magana a taron, ya na kira ga jama’a su zabi PDP, tare da rokon hukumar INEC ta shirya zabe na kwarai.

Sauran gwamnonin PDP da su ka halarci taron sun hada da Douye Diri, Seyi Makinde, Bala Mohammed, Ifeanyi Okowa da mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel