Dan majalisa daga Zamfara ya bayar da tallafi na miliyoyin naira ga al'umman mazabarsa (hotuna)

Dan majalisa daga Zamfara ya bayar da tallafi na miliyoyin naira ga al'umman mazabarsa (hotuna)

- Wani mamba a majalisar wakilai mai wakiltan yankin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, Kabiru Mai-Palace, ya tallafawa al'ummansa

- Ya rarraba masu kayayyakin tallafi da suka hada da dutsen guga na gawayi, sabulun wanki da sauransu domin fara sana’a

- Hakan ya sa jama'a da dama sun tofa albarkacin bakunansu

Dan majalisar wakilai na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Kabiru Mai-Palace, ya kaddamar da wani shirin tallafi na miliyoyin naira a mazabarsa da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

An kaddamar da shirin ne a garin Tsafe inda wadanda suka amfana suka samu kayayyaki irin su manyan baho, dutsen guga na gawayi, sabulun wanki da sauransu domin fara sana’a.

Jaridar Vanguard ta wallafa hotunan kayayyakin tallafin kamar haka:

Dan majalisa daga Zamfara ya bayar da tallafi na miliyoyin naira ga al'umman mazabarsa (hotuna)
Dan majalisa daga Zamfara ya bayar da tallafi na miliyoyin naira ga al'umman mazabarsa Hoto: Vanguard
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun bazama bincike a kan lamarin matashin da ya soka wa kansa wuka har lahira saboda budurwa a Kano

Ga wasu daga cikin martanin da wasu mabiya shafinmu na Facebook suka yi:

Mannir Umar: "Mai talaka zai da wani baho, da gawayi da dutsan guga, Wannan shine romon dimukuradiyyar, Allah ya Kara Fahimtar da talakawa."

M.N. Usman: "Allah yasaka mai da alkhairi, yabashi ikon yin abun da yafi wannan nan gaba, Ameen."

Amin M. Kamil: "Kai!!! Wannan dutsen gugan ai na mugunta ne, nauyi ma kawai zai sheqe mutum !!!"

Hassan Boothcut: "Mutane sunada matsala wlh. Yanxu wannan abun da yayi ai abun a yaba masa ne sbd abunda kake ganin kafi karfi wani kuma kokowa suke."

Real Mubarak Musa-elhassan: "Kenan kowa yakoma wanki da Guga?"

Dayyab KD: "Alhamdulillah wannan tsari ne mai kyau ataimakawa talaka tundaga ƙasa. Shine zakaga talaka yana walwala cikin farin ciki. Hon Kabiru Maipalace. Taimakonshi TALAKAWA yadaɗe yanayi tundaga matakin farko."

Muhammad Sani: "Kasarmu tagadon gado nigeria mai abun mamaki."

Abdurrahman Lawan Ahmad Nguru: "Tir Allah Kyauta Wanan wanne irin zalincine Haka idan mutom yazo da cewa kamai temako Akan Wanan abun daka bayar saika Masa Amma Kano kayi Wanan aikin kace ka kyautatawa Alummar ka Dan uwana gaskia Ina. Allah Allah yabada sa,a amen."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel