Jami’an tsaro sun tsare Dalibin da ya bude shafin Twitter na Goodluck Jonathan

Jami’an tsaro sun tsare Dalibin da ya bude shafin Twitter na Goodluck Jonathan

Wani ‘dalibin jami’ar fasaha ta the Ladoke Akintola da ke garin Ogbomoso, wanda ake zargi da laifin bude shafin Twitter da sunan Jonathan ya shiga hannn hukuma.

Jaridar Punch ta ce jami’an ‘yan sanda na CID da ke hedikwatar Abuja su na cigaba da tsare Babatunde Olusola a dalilin gaza cika sharudan beli da ya yi.

Rahoton da jaridar ta fitar a ranar 25 ga watan Yuli ya bayyana cewa Mista Olusola ya shafe watanni biyu a rufe, kuma an hana shi ganawa da lauyoyin da su ka tsaya masa.

Wani lauya kuma ‘dan gwagwarmaya, Tope Akinyode, ya fadawa jaridar cewa ya yi yunkurin ganawa da matashin, amma jami’an ‘yan sandan da ke FCID a Abuja sun hana shi.

Lauyan ya ke cewa: “Sau biyu ana hana ni ganin Olusola a makon da ya wuce. An fada mani cewa sai babban jami’in da ke bincike, IPO, ya bada izni kafin in iya ganinsa.”

“Babu dokar da ta ce sai Lauya ya samu izni daga IPO kafin ya ga wanda ya ke tsayawa wa. Wannan abin tir ne, kuma dole a daina haka. Za mu kalubalanci hakan.”

KU KARANTA: Bene ya duro ya rutsa da wasu mutane a Abuja

Jami’an tsaro sun tsare Dalibin da ya bude shafin Twitter na Goodluck Jonathan
Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan Hotp: Facebook
Asali: Facebook

Akinyode ya yi magana game da haduwarsu ta karshe: “Lokacin da na yi magana da shi karshe, ya fada mani bai da lafiya, ya na fama da alamun Coronavirus. Hankali ya tashi sosai saboda wani mutumin kasar Sin da ya ke tsare mai suna Mista Wan ya kamu da kwayar cutar.”

Wannan Lauya ya ce kafin nan, Babatunde Olusola bai jin dadi tun da jami’an tsaro su ka dauke shi daga Ogbomoso zuwa Ibadan inda ya rika barci a cikin bawali a ofishin SARS.

“Wannan ya na cikin mayuwacin halin da ya shiga.”

Daga baya an fahimci cewa Mista Oluola bai da iyaye kuma bai iya kawo wani babban jami’in gwamnati da ya kai matakin aiki na 15 da zai karbi belinsa ba.

Ana zargin Olusola da rajisatar wani akawu mai sunan @jayythedope, wanda ya ke yi wa tsohon shugaban Najeriya Dr. Goodluck Jonathan shakiyanci da shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel