An yi musayar wuta tsakanin magoya bayan APC da PDP a Edo

An yi musayar wuta tsakanin magoya bayan APC da PDP a Edo

Wasu 'yan daba da ake zargin suna goyon bayan dan takarar jam'iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, sun gwabza da 'yan dabar da ke goyon bayan gwamna Godwin Obaseki, dan takarar jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Gungun 'yan dabar sun fafata a daura da fadar sarkin Benin, Oba Ewuare II, a ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi musayar wuta yayin fafatwar 'yan dabar, lamarin da ya haifar da rauna jama'a tare da lalata ababen hawa.

Rikicin ya barke ne lokacin da gwamna Obaseki tare da sauran gwamnonin jam'iyyar PDP suka ziyarci fadar sarkin gabanin kaddamar da yakin neman zaben Obaseki a matsayin gwamnan jihar Edo a karo na biyu.

Wata majiya ta bayyana cewa rigimar ta balle ne bayan gwamnan da tawagarsa sun bar fadar, sannan an fi yiwa bangaren jam'iyyar PDP barna saboda magoya bayan jam'iyyar APC sun fisu yawa.

An yi musayar wuta tsakanin magoya bayan APC da PDP a Edo
Gwama Obaseki
Asali: Twitter

Majiyar ta kara da cewa magoya bayan PDP sun garzaya filin wasan tamaula na Ogbe, wurin taron jam'iyyar, inda suka nemi gudunmawar abokansu domin ramuwar gayya a kan magoya bayan jam'iyyar APC.

Majiyar jaridar Daily Trust ta sanar da ita cewa an raunata magoya bayan kowacce jam'iyya, sannan an lalata motoci.

DUBA WANNAN: Da duminsa: An hana Magu gabatar da hujjoji gaban kwamitinin bincike

Sai dai, daga bisani jami'an 'yan sanda sun kawo dauki tare da kwantar da rikicin.

Da yake magana a kan rikicin da aka yi a tsakanin magoya bayan APC da PDP, gwamna Obaseki ya gargadi magoya bayansa da su kasance masu zaman lafiya a duk inda suka samu kansu.

"Ba ma son zubar da jini."

"Kar ku dauki fansa amadadinmu"

"Burinsu shine su tsorata jama'a," a cewar Obaseki.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, DSP Chidi Nwanbuzor, bai samu ba saboda bai amsa kira ba lokacin da manema labarai suka kirashi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel