Yadda rundunar soji ta kama manyan 'yan bindiga 6 a Sokoto
Dakarun rundunar soji da ke aiki a karkashin atisayen 'SAHEL SANITY' suna cigaba da samun gagarumar nasara a kokarinsu na kawo karshen aiyukan 'yan bindiga da ke satar shanu, garkuwa da mutane, da aikata sauran aifuka.
A ranar 18 ga watan Yuli ne dakarun rundunar soji suka kama wasu 'yan bindiga biyu; Marti Abdullahi da Abdullahi Muazu, a kauyen Gundumi da ke karamar hukumar Isah a jihar Sokoto.
A cikin wata sanarwa da rundunar soji a yau, Alhamis, ta ce ta kama 'yan bindigar bayan samun sahihan bayanai a kan al'amuransu.
Sanarwar ta bayyana cewa dakarun rundunar soji sun sake kama wasu gagararrun 'yan bindiga biyu; Gabbe Muhammad da Muhammad Bello, a kauyen Mai Filoti da ke yankin karamar Sabon birni a jihar Sokoto.
Gaabbe da Bello sun kasance sanannu a bangaren garkuwa da mutane da kuma fashi da makami, kamar yadda rundunar soji ta bayyana.
Kazalika, dakarun rundunar soji da ke aiki a jihar Katsina sun samu nasarar kama wasu 'yan bindiga biyu; Mohammed Lawal da Useni Abubakar, a kauyen Nahuta da ke karamar hukumar Batsari.
Mazauna Nahuta sun sanar da rundunar soji cewa masu 'yan bindigar sun jagoranci kai hare - hare kauyukan a lokuta daban - daban.
Rundunar soji ta kara da cewa dakarunta sun kara kama wani dan bindiga a kauyen Yar Tasha tare da bayyana cewa yanzu haka ana neman sauran abokansa da suka kirashi a waya bayan ya shiga hannu.
A cewar rundunar soji, dukkan 'yan bindigar da aka kama suna tsare a hedikwatarta domin amsa tambayoyi kafin a mikasu zuwa hannun hukumar 'yan sanda domin gurfanar dasu a gaban kotu.
A karamar hukumar Kankara da ke jihar Katsina, rundunar soji ta ce ta kwace shanu 8 daga hannun wasu 'yan bindiga da suka gudu bayan sun samun labarin zuwan rundunar soji.
DUBA WANNAN: Guguwar Buhari ba zata yima aiki a 2023 ba, APC ta gargadi mambobinta
An yi musayar wuta tsakanin dakarun rundunar soji da wasu 'yan bindiga da suka yi garkuwa da wani mutum mai suna Nuhu Gambo a Unguwar Tabo da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Bayan sun ga babu alamun nasar, 'yan bindigar sun gudu daga maboyarsu da ke dajin Rangwada tare da barin baburansu guda uku.
Dakarun rundunar soji sun sake kwace shanu 25 daga wurin wasu 'yan bindiga da suka gudu bayan jama'ar kauyen Zauni a yankin Magami a karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
A ranar 22 ga watan Yuli, dakarun rundunar soji sun sake kama wasu 'yan bindiga biyu da babura 5 a Mara Runka.
'Yan bindigar sun gudu sun bar kayayyakinsu bayan sun fahimci cewa ba zasu ci riba ba a musayar wutar da suka fara da sojoji.
Rundunar soji ta ce dakarunta a karkashin atisayen 'SAHEL SANITY' suna cigaba da sintiri a jeji da sauran maboyar 'yan ta'adda a yankin arewa maso yamma domin bawa manoma damar samun aiki a gonakinsu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng