Kaye a zaben fidda gwanin PDP: Mataimakin gwamnan Ondo ya yi martani
- Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi, ya yi martani a kan nasarar Eyitayo Jedege a matsayin dan takarar gwamnan PDP a zaben Oktoba
- Ajayi ya ce ya yi kokari iyakar kokari amma akwai wasu tawaga da suka hana shi nasarar zama dan takarar jam'iyyar adawar
- Hakan ya zama biyu babu kenan domin a yanzu zai fuskancin matsi na neman ya yi murabus daga kujerarsa kasancewar ya bar APC
Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi, ya yi martani a kan nasarar Eyitayo Jedege a matsayin dan takara a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben gwamnoni na watan Oktoba mai zuwa.
Ajayi ya ce ya yi kokari iyakar kokari amma akwai wasu tawaga da suka hana shi nasarar zama dan takarar jam'iyyar adawar.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, wani babban lauya da ke garin Ipele, kusa da Owo, ya kayar da Ajayi da wasu mutum shida a zaben fidda gwani da aka yi.
An yi zaben fidda gwanin ne a Dome da ke Akure, babban birnin jihar.
Tsohon Antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar, ya samu kuri'u 888 yayin da mataimakin gwamnan ya samu kuri'u 657.
Jegede ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani a karkashin jam'iyyar PDP a 2016 kuma ya karbi tikitin takarar gwamnan jihar inda ya yi hamayya da Gwamna Rotimi Akeredolu na jam'iyyar APC.
A yayin martani a kan rashin nasararsa, a wata takarda da Ajayi ya fitar ta hannun mai bashi shawara a kan kafafen yada labarai, Allen Sowore, ya ce:
"Jama'a sun yi magana kuma mun amince da hakan. Muna yi wa jama'ar jihar Ondo fatan alheri tare da wanda yayi nasara."
'Yan takara takwas ne suka fito zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP.
KU KARANTA KUMA: Ka fito da shaida a kan cewa ina karbar rashawa - Magu ya kalubalanci Malami
Sune Agboola Ajayi, Eyitayo Jegede, Boluwaji Kunlere, Eddy Olafeso, Ben Okunomo, Bode Ayorinde, Godday Erewa da Sola Ebiseeni.
Ajayi, mataimakin gwamnan jihar Ondo, ya fice daga jam'iyyar APC kuma ya koma jam'iyyar PDP da burin samun tikitin jam'iyyar adawar.
Rashin nasarar shi ake kira da biyu babu don a yanzu zai fuskanci yadda zai sauka daga zama mataimakin gwamnan jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng