Ka fito da shaida a kan cewa ina karbar rashawa - Magu ya kalubalanci Malami

Ka fito da shaida a kan cewa ina karbar rashawa - Magu ya kalubalanci Malami

Dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Ibrahim Magu, ya kalubalanci Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami.

Ya bukaci da ya nuna wata alamar da ke bayyana cewa ta damfara ya kudantar da kanshi da kuma cewa yana karbar cin hanci don bai wa wandanda ake zargi kariya.

Magu ya kalubalanci Malami ne a yayin da yake amsa tuhumar kwamitin fadar shugaban kasa da ke bincikar sa a kan rashawa da kuma ayyukansa da Malami ya koka a kai.

A makon da ya gabata, Malami ya sanar da dakatar da Magu bayan amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kwamitin fadar shugaban kasa wanda ya samu shugabancin Ayo Salami, tsohon babban Alkalin kotun daukaka kara, ke bincikar Magu a kan zargin cin rashawa da rashin biyayya da Malami ya koka a kai.

Ka fito da shaida a kan cewa ina karbar rashawa - Magu ya kalubalanci Malami
Ka fito da shaida a kan cewa ina karbar rashawa - Magu ya kalubalanci Malami Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An tsaresa na tsawon kwanaki 10 kafin a sako shi.

Bayan kama shi, an zargi Magu da waskar da biliyoyin naira da aka samo daga mahandaman kasar nan tare da wafce ruwan da kudin ke kawowa.

Kamar yadda Premium Times ta ga martanin Magu, ya musanta zargin da ake masa na cewa yana karbar cin hanci tare da wasu jami'an hukumarsa.

"Wannan zargin abin takaici ne, sharri ne, kage ne da kuma yunkurin bata min sunana da na dade ina ginawa," yace.

"Ba kamar yadda zargin ya bayyana ba, na san ban ci ko sisin kwabo daga kudin da aka samo ba don amfanin kaina. Ina kalubalantar mai zargin da ya fitar da shaida a kan damfarar da yake zargina da ita."

Magu ya ce ikirarin da Malami ya yi na cewa ya samu koke masu tarin yawa a kan amfanin da yake da ofishinsa ba ta yadda ya dace ba wajen azurta kanshi.

KU KARANTA KUMA: Katsina: 'Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi garkuwa da mutum 17

"A kokarin da nayi a matsayin mukaddashin shugaban hukumar EFCC, na tashi tsaye wurin tabbatar da cewa na yaki rashawa a Najeriya.

"Amma kuma wasu wadanda ake zargi ko ake bincike sun hada kai wurin yaka ta da zargin na karya mai iya kawo gaba.

"Ban taba amfani da ofishina ba ta yadda ya dace ba. Ban taba kokarin ganin azurta kaina ba yayin da nake ayyuka na. Ina kalubalantar wanda ke zargina da ya fitar da shaida kowacce iri ce a kan zargin da yake min," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng