Katsina: 'Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi garkuwa da mutum 17

Katsina: 'Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi garkuwa da mutum 17

- 'Yan bindiga sun kai farmaki a kananan hukumomi 3 na jihar Katsina ya yi sanadin mutuwar mutane biyu

- Har ila yau an kuma yi garkuwa da mutane 17 da kuma satar dabbobi masu tarin yawa

- Hakimin garin, Malam Tukur, ya yi kira ga mazauna kauyen da su dauki hakan a matsayin kaddara kuma ya yi alkawarin kiran jami'an tsaro

Hare-haren 'yan bindiga a kananan hukumomi 3 na jihar Katsina ya yi sanadin mutuwar mutane biyu, garkuwa da mutane 17 da kuma satar dabbobi masu tarin yawa.

A kauyen Kandawa na karamar hukumar Batsari, mutane biyu sun rasa rayukansu. Mazauna yankin sun gano cewa Malam Basiru da Sanusi Dan Almajir ne suka rasu.

Daga bisani an kai gawarsu fadar hakimi a yayin zanga-zanga, jaridar Dily Trust ta ruwaito.

Hakimin garin, Malam Tukur, ya yi kira ga mazauna kauyen da su dauki hakan a matsayin kaddara kuma ya yi alkawarin kiran jami'an tsaro.

Hakan ne yasa suka koma don birne gawawwakin.

Katsina: 'Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi garkuwa da mutum 17
Katsina: 'Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi garkuwa da mutum 17 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Har a halin yanzu, 'yan sanda basu yi martani a kan aukuwar lamarin ba.

Hakazalika, a ranar Laraba, mata 17 aka sace a kauyen Zakka da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Aisha Umaru, bahaushiyar farko da ta fara shiga shirin BBNaija ta fara shan suka

Amma kuma kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce mutum tara ne ba a gani ba don an samu ceto mutane 8 da taimakon tubabbun 'yan bindiga da 'yan sanda.

A wani ci gaba makamancin hakan, an kai hari kauyen Damari da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina a sa'o'in farko na ranar Litinin inda aka yi awon gaba da sama da shanu 40.

A wani labari na daban, Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya je fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke Abuja a ranar Litinin.

Buratai ya je bayyanawa shugaban kasar inda aka kwana a wurin yaki da rashin tsaro.

A yayin ganawa da manema labarai bayan taron, ya ce domin shawo kan wannan matsalar, dole ne dukkan 'yan Najeriya su hada kai wurin yaki da ta'addanci.

Ya ce duk da ta'addanci sabon abu ne a kasar nan, rashin tsaro ya dade amma abu mafi muhimmanci shine yadda za a shawo kan shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel