Majalisar Wakilai za ta binciki CBN a game da bashin rage radadin COVID-19

Majalisar Wakilai za ta binciki CBN a game da bashin rage radadin COVID-19

A ranar 22 ga watan Yuli, 2020, jaridar Punch ta rahoto cewa majalisar wakilan tarayya ta cin ma matsaya cewa za ta yi bincike a babban bankin CBN.

‘Yan majalisar wakilan za su binciki babban bankin ne a dalilin zargin wahalar da mutane su ke sha wajen karbar bashin da bankin ya warewa kananan ‘yan kasuwa.

Wani ‘dan majalisa, Honarabul Ahmadu Usman Jaha ya ce masu kanana da matsakaicin kasuwanci su na kukan cewa ba su iya karbar aron kudin da CBN ta ke badawa.

Ahmadu Usman Jaha ya ke cewa akwai bukatar a binciki bangaren tattalin babban bankin kasa na CBN da kuma tsarin da aka kawo na bada bashi ga masu aikin gona.

Ganin halin da annobar cutar COVID-19 ta jefa Bayin Allah, Bankin CBN ya kawo tsare-tsare domin rage radadin halin da marasa karfi su ka shiga a Najeriya.

Bayan Ahmadu Jaha mai wakiltar Damboa/Gwoza/Chibok na jihar Boro a majalisar wakilai ya yi jawabi, abokan aikinsa sun taru sun yi na’am da maganar da ya kawo.

KU KARANTA: Najeriya za ta karbo bashin N4tr a kasafin kudin 2021

Majalisar Wakilai za ta binciki CBN a game da bashin rage radadin COVID-19
Babban bankin Najeriya
Asali: UGC

Majalisar wakilai ta amince da kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki bangaren tattali na CBN wanda shi ne babban bankin Najeriya.

Wani ‘dan majalisa har wa yau, ya yi amfani da wannan dama ya koka da yadda annobar COVID-19 ya kawo cikas ga ‘yan kasuwar da ke shigo da kaya daga kasashen waje.

Hon. Christopher Okwudili ya gabatar da kudiri da ya ce ya zama dole a ceci irin wadannan rukuni na ‘yan kasuwa daga burmawa cikin karayar tattalin arziki.

Bayan nan, majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya a karkashin tsare-tsaren rage radadin annobar COVID-19, ta ceci masu fatauci da su ka shiga cikin mawuyacin hali.

Majalisar kasar ta daurawa kwamitin kasuwanci alhakin bincike a game da lamarin. Za a saurari rahoton binciken nan da makonni biyu domin ayi abin da ya dace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel