Tattalin arziki: Gwamnatin Tarayya ta na sa ran cin bashin N4tr a shekarar badi

Tattalin arziki: Gwamnatin Tarayya ta na sa ran cin bashin N4tr a shekarar badi

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kawo maganar batar da Naira tiriliyan 12.66 a matsayin kasafin kudin shekara mai zuwa na 2021.

Kasafin kasar da ake shiryawa zai zo da gibin Naira tiriliyan 5.16. Hakan na nufin dole gwamnati ta nemo hanyar da ta samu cikon wadannan kudi.

Rahoton da jaridar Punch ta fitar a ranar 21 ga watan Yuli, 2020, ya bayyana cewa dole Najeriya za ta nemo bashin Naira tiriliyan 4.28.

Gwamnatin kasar wanda ta dogara da arzikin man fetur za ta fito da ragowar gibin da za a samu ne daga harajin da za a tatsa a cikin gida.

Wannan lissafi da aka yi duk ya na cikin takardar MTEF/FSP na tsarin tattalin arzikin kasar wanda zai yi aiki tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023.

A ranar Talatar nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da MTEF/FSP gaban majalisar tarayya domin su amince da tsare-tsarensa na kashe kudi.

KU KARANTA: FEC ta yi na'am da kashe N75b a kan matasan Najeriya

Tattalin arziki: Gwamnatin Tarayya ta na sa ran cin bashin N4tr a shekarar badi
Shugaba Buhari Hoto: FEC
Asali: Facebook

A kasafin kudin na shekarar badi, gwamnati ta na hangen Naira tiriliyan 5.75 a matsayin kudin da za a batar a kan albashi da tafiyar da gwamnatin tarayya.

Bayan haka kuma Naira tiriliyan 3.12 za su tafi a biyan bashin da ake bin kasar. A daidai wannan lokaci kuma za a nemi karbo wani sabon bashi na Naira tiriliyan 4.2.

A 2021, daya bisa ukun kasafin kudin da aka tsara zai fito ne daga bashin da za a ci. Kwanakin baya majalisa ta fito ta ce bashin da ke kan Najeriya ya kai Tiriliyan 33.

A kasafin, ana lissafin fiye da Naira biliyan 200 su fito ta hanyar saida wasu kadarorin gwamnati. Batun saidawa ‘yan kasuwa kadarori ya kan jawo ce-ce-ku-ce a majalisa.

A halin yanzu ana jira majalisa ta amince da MTEF/FSP, nan gaba kuma za a gabatar da ainihin kundin kasafin kudin kasar, wanda ba a taba ganin irinsa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng