Sarkin Gabas ya ajiye rawani saboda an nada Fani-Kayode Sadaukin Shinkafi

Sarkin Gabas ya ajiye rawani saboda an nada Fani-Kayode Sadaukin Shinkafi

Tijjani Salihu Shinkafi, wani mai rike da sarautar gargajiya a masarautar Shinkafi, ya yi gajeren murabus a dalilin sarautar da mai martaba Sarki ya ba Femi Fani-Kayode.

A ranar Litinin, Sarki Alhaji Muhammad Makwashe ya sanar cewa Femi Fani-Kayode zai zama sabon Sadaukin Shinkafi. Wannan mataki da aka dauka bai zo wa mutane da-dama da dadi ba.

Daga cikin wadanda su ka yi tir da wannan nadi da ake nema ayi har da Sarkin Gabas Shinkafi, Tijjani Salihu Shinkafi wanda babban malami ne a jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto.

Dr. Tijjani Salihu Shinkafi ya ce ya tube rawaninsa na Sarkin Gabas har sai lokacin da Mai martaba Sarkin Shinkafi ya janye wannan sarauta da ya ba Mista Femi Fani-Kayode.

Da ya ke bayani a shafinsa na Facebook, Salihu Shinkafi ya na ganin cewa bai dace ya cigaba da rike sarauta a masarautar da ta karrama makiyin Daular Usmaniyya da ake tinkaho da ita ba.

Basaraken ya ke cewa sarautar Sadaukin Shinkafi ta tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa ce, amma ya ce masarautar ta yi watsi da wannan, ta buge da kwadayin kudi.

KU KARANTA: Munanan ayyuka 3 da 'Yan Arewa su ke yi a kasar nan - FFK

Sarkin Gabas ya ajiye rawani saboda an nada Fani-Kayode Sadaukin Shinkafi
Femi Fani-Kayode
Asali: Depositphotos

Mai dakin gwamnan jihar Kebbi. Dr. Zainab Shinkafi-Bagudu ta zargi masarautar Shinkafi da neman abin Duniya. Dr. Shinkafi ta nuna cewa hakan abin Arewa ta koka ne.

Shinkafi ya ce tsohon ministan kasar ya ziyarci garin Maradun a makon da ya gabata, amma Sarkin kasar bai zabi ya ba shi sarauta ba duk da cewa nan ne mahaifar gwamna mai-ci.

Ya ce ba yaki da Femi Fani-Kayode ko Yarbawa ko Kiristoci ke yi ba, sai dai ya ajiye rawani ne saboda kokarin kare martabar Daular. A cewarsa bai yi tunanin Kayode zai karbi sarautar ba.

A dalilin haka ne mutane su ka rika kira ga masarutar Shinkafi ta janye wannan nadi da ta yi.

A cewarsa idan wannan zanga-zanga da ya yi, ta yi nasara, masarautar Shinkafi za ta dawo da darajar ta. Wannan shi ne ra’ayin kungiyar AYCC ta wasu matasan Arewacin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng