Akwai yiwuwar Tukur Buratai da Mahadi Shehu su shiga kotu kan zargin N250m

Akwai yiwuwar Tukur Buratai da Mahadi Shehu su shiga kotu kan zargin N250m

- Shugaban Hafun Sojoji ya na tunanin kai karar ‘dan kasuwa gaban Alkali

- Tukur Buratai ya musanya zargin karbar N250m daga gwamnatin Katsina

- Babban Sojan ya bukaci Mahadi Shehu ya janye wannan magana da ya yi

A ranar Talata, 21 ga watan Yuli, 2020, shugaban hafsun sojojin kasa, Tukur Yusuf Buratai, ya yi magana game da zargin da ake yi masa na karbar kudi daga hannun gwamnatin Katsina.

Shugaban hafsun sojojin kasan na Najeriya ya bukaci wanda ya fara yada wannan jita-jita watau Alhaji Mahadi Shehu, ya fito ya janye kalamansa, sannan ya nemi afuwarsa.

Janar Tukur Yusuf Buratai ya na bukatar Mahadi Shehu wanda attajirin ‘dan kasuwa ne da ke zaune a garin Kaduna da ya lashe aman da ya yi a gidajen jaridu uku da ke jihar Katsina.

Jaridar Punch ta ce hafsun sojan ya yi wannan magana ne ta bakin lauyansa, Usuagwu Ogochukwu a wajen wani taro da ya kira da ‘yan jarida a Katsina.

Shehu ya ce gwamnatin jihar Katsina ta na ikirarin ta ba Janar Tukur Buratai kudi N250m a matsayin kudin walwala domin kafa wata bataliyar sojojin kasa a Nuwamban 2017.

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina ta batar da N24b daga asusun kudin tsaro

Akwai yiwuwar Tukur Buratai da Mahadi Shehu su shiga kotu kan zargin N250m
Shugaban hafsun sojojin kasa Tukur Buratai
Asali: Facebook

Buratai ya ce babu gaskiya a wannan zargi mai nauyi wanda aka kirkira ba tare da hujja ba.

Kafin yanzu gwamnatin Katsina ta bakin sakataren jihar watau Mustapha Muhammad Inuwa, ta karyata wannan zargi da ‘dan kasuwar ya fito gaban Duniya da ya yi.

Barista Usuagwu Ogochukwu, lauyan Janar Tukur Yusuf Buratai ya ba ‘dan kasuwar sa’a 48 ya fito ya bada hakuri a gidajen jaridu, idan kuma ba haka ba ya shirya zuwa kotu.

Hafsun sojin ya nuna cewa Mahadi Shehu zai fuskanci shari’a a kotu inda za a nemi ya yi kashin Naira biliyan 10 a dalilin batawa COAS suna da aka yi ba tare da hakki ba.

“Idan ba haka ba zan shigar da karar kage a kansa, kuma zan bukaci kudi Naira biliyan 10 domin bata suna, kuma wannan bai kunshi karar da jami’an tsaro za su shigar a kansa.” inji Lauyan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng