An yi bikin ƙara wa 'yan sanda 10 girma a Abuja

An yi bikin ƙara wa 'yan sanda 10 girma a Abuja

Babban Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya ce an yi wa jami'an 'yan sanda ƙarin girma wanda yawansu ya kai 41,863 a cikin watanni 19 da suka gabata.

Mista Adamu ya fayyace hakan ne a ranar Litinin yayin bikin ɗaga likafar wasu mayan jami'an 'yan sanda 10 da aka gudanar a Abuja, babban birnin kasar.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito Adamu ya ce: "Tun daga lokacin da na karbi akalar jagoranci ta hukumar 'yan sandan Najeriya a watan Janairun 2019, an yi wa jami'an 'yan sanda 41,863 zuwa matsayi na gaba.

Ya ce tsarin ɗaga likafar jami'an wata dabara ce ta kara wa jami'an karfin gwiwa da kuma karsashin ma'aikata wajen matsalolin tsaro na cikin gida.

Yayin bikin ƙara wa 'yan sanda 10 girma
Hoto daga Hukumar 'Yan sandan Najeriya
Yayin bikin ƙara wa 'yan sanda 10 girma Hoto daga Hukumar 'Yan sandan Najeriya
Asali: UGC

Mista Adamu ya ce ana gudanar da shirin ɗaga likafar ma'aikatan ne bisa la'akari da tsari da kuma cancanta gami da kwarewa da kwazo a kan aiki.

Babban sufeton 'yan sandan ya ce wannan karin girma da aka yi wa manyan jami'ai 10 a yanzu, ya biyo bayan wanda aka yi a baya bayan nan inda aka ɗaga likafar jami'ai 6,601.

Daga cikin manyan ma'aikata da aka yi karin girma a baya bayan nan sun hada da DIG daya, AIG hudu, Kwamishionini (CP) 3, Mataimakan Kwamishinoni (DCP) 3 da Manyan Sufirtanda (CSP) takwas.

Sauran sun hada da Sufirtanda (SP) 607, Mataimakan Sufirtanda (DSP) 206 da kuma ASP guda 5,769.

KARANTA KUMA: Likita ta mutu a Ribas kwana biyu da kammala hidimar kasa

Mista Adamu wanda ya yi wa sabbin manyan ma'aikatan kwalliyar ɗaga likafa, ya nemi da su jajirce wajen nuna kwarewa wajen zartar da duk wani hukunci yayin aiki a koda yaushe.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, ya halarci bikin yi wa jami'an 'yan sandan ƙarin girma.

Sakataren gwamnatin kasar ya taya ma'aikatan murna tare da jan kunnensu a kan daukar izina ta wannan karin girma da suka samu a matsayin kira na kara zage dantse wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel