Ya kamata Ahmad Lawan ya jarraba sa’arsa a zaben 2023 – inji Mutanen Oke
Ganin ana dumfarar 2023, shekarar da za a sake gudanar da zabe a Najeriya, wasu manya daga yankin Oke sun dura majalisa, su na kiran Ahmad Lawan ya fito takara.
Wadannan mutane na shiyyar Oke a yankin Ogun da Oyo, su na rokon shugaban majalisar dattawan ya fito takarar shugaban kasa ne a zaben 2023.
A ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, wasu daga cikin sarakunan gargajiya da ‘yan siyasar yankin yarbawa su ka kai wa Ahmad Lawan ziyara ta musamman a ofishinsa.
Manyan mutanen na Oke sun gana da shugaban majalisar tarayyar ne bayan an yi wani zama a zauren majalisar inda aka saurari kudirin kafa jami’a a garin Oke.
Wasu daga cikin mutanen Ogun da Oyo sun halarci zaman da aka yi domin sauraron kudirin kafa jami’ar aikin gona da fasaha a garin Ole, inda ake fama da karancin makarantu.
Jama’a su na cigaba da wannan kira ne a daidai lokacin da Lawan ya fito ya na fatali da yunkurin da wasu su ke yi na ganin sun tunzurasa ya fito takarar shugaban kasa.
Sanata Ahmad Lawan ya ce babu lissafin 2023 a gabansa a halin yanzu da ya kamata ace an maida hankali wajen shawo kan matsalolin da su ka dabaibaye kasar nan.
KU KARANTA: Buhari da Jonathan su na kus-kus a Aso Villa
Da ya ke magana a madadin al’ummar Oke – Ogun, Barista Ahmed Raji SAN, ya fadawa shugaban majalisar cewa jama’a za su yi farin cikin ganin an kafa jami’ar tarayya a Oke.
Haka zalika Ahmed Raji ya ce za su yi sha’awar ganin Lawan ya kawo ziyara a matsayin babban bako zuwa wannan makaranta wata rana idan an amince da a gina makarantar.
Raji ya fadawa Lawan cewa ”Mu na bibiyar tafiyar siyasarka a ‘yan shekarun nan daga zaman ka a majalisar wakilai zuwa majalisar dattawa, an ga amfaninka, ka bar tarihi.”
“Mutanen Oke – Ogun su na so ka yi amfani da damar ka wajen ganin kudirin kafa jami’ar aikin gona da fasaha na tarayya ya zama doka kuma an tabbatar da hakan.”
Wadanda su ka halarci zaman sun hada da Sanata Buhari, ‘yan majalisar yankin da sauran manyan 'yan siyasa da ake ji da su irinsu tsohon minista Adebayo Shittu.
Sarakunan da ke wurin taron su ne : Okere na Shaki, Sarki Khalid Olabisi Oyeniyi, Abdul Ganiyu Adekunle Salau. Manyan sun bukaci Lawal ya fito takara a babban zaben 2023.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng