Ronaldo ya zama ‘Dan wasan farko da ya ci kwallaye 50 a Ingila, Sifen, da Italiya

Ronaldo ya zama ‘Dan wasan farko da ya ci kwallaye 50 a Ingila, Sifen, da Italiya

- Cristiano Ronaldo ya ci kwallonsa na 50 a gasar Seria A a karawarsu da Lazio

- ‘Dan wasan ya zama wanda ya ci kwallaye 30 a Juventus a karon farko tun 1952

- Tauraron shi ne ‘dan wasan da ya fara cin kwallaye 50 a Seria A, La-liga da BPL

Idan mu ka koma bangaren wasan kwallon kafa, za mu ji cewa Cristiano Ronaldo ya fara rubuta sunansa da tawadar gwal a kungiyar Juventus, kasar Italiya.

A wasan jiya Litinin, 20 ga watan Yuli, 2020, ‘dan wasan gaba Ronaldo mai shekaru 35 ya zura kwallaye biyu a gwabzawar Juventus da kungiyar Lazio.

A wannan wasa ne Ronaldo ya ci kwallonsa na 50 a gasar Seria A, hakan na zuwa ne shekaru biyu da zuwansa kasar Italiya bayan tashinsa daga kungiyar Real Madrid.

Da wannan tarihi da ‘dan wasan ya kafa, ya zama ‘dan kwallon da ya fi kowa saurin jefa kwallaye 50 a gasar (a zuwa 61), ya sha gaban Shevchenko, Ronaldo da Trezeguet.

KU KARANTA: Babu wanda zai lashe kyautar Ballon D' or a shekarar 2020

Ronaldo ya zama ‘Dan wasan farko da ya ci kwallaye 50 a Ingila, Sifen, da Italiya
Ronaldo ya ci kwallaye 30 a Seria A
Asali: UGC

Andriy Shevchenko ya iya cin kwallaye 50 ne bayan wasanni 68, shi kuwa De Lima ya ci kwallo 50 ne a wasansa na 70, abin da ya dauki David Trezeguet da Diego Milito wasanni kusan 80.

Ronaldo ya zama ‘dan wasa na uku a tarihin Juventus da ya ci kwallaye 30 a shekara guda. Kafin yanzu Felice Borel da John Hansen ne kadai su ka shiga cikin tarihin kungiyar.

Akwai yiwuwar Ronaldo ya karya tarihin Felice Borel wanda ya ci kwallaye 31 a 1933, ya kuma zama daidai da John Hansen wanda ya yi irin wannan namijin kokari a 1952.

Ba a nan kurum tarihin da Cristiano Ronaldo ya karya ya tsaya ba, a daren na jiya, ya zama ‘dan wasan farko da ya ci kwallaye 50 a kasashen Ingila, Sifen da Italiya.

Tsohon ‘dan wasan na Manchester United da Real Madrid shi ne ‘dan kwallon farko a Duniya da ya zura kwallaye har 50 a Seria A, La-liga da kuma Firimiya.

A shekaru biyu, Ronaldo ya hadu da kungiyoyi 21 a Seria A, ya zurawa dukkansu kwallo a raga face Chievo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel