Zaben Edo: Oshiomhole ya sha alwashin tsige Obaseki daga kujerarsa

Zaben Edo: Oshiomhole ya sha alwashin tsige Obaseki daga kujerarsa

- Tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole, ya ba magoya bayan jam’iyyar tabbacin nasara a zaben gwamnan Edo mai zuwa

- Oshiomhole ya sha alwashin tsige Gwamna Godwin Obaseki daga kujerarsa na zaben Satumba

- Ya ce Allah ya fitar da macijin da ke gidansu zuwa inda ya cancanta

Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ya ba magoya bayan jam’iyyar tabbacin nasara a zaben gwamnan Edo mai zuwa.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a Edo a karshen mako, ya nuna karfin gwiwar cewa APC za ta yi nasara a zaben ranar 19 ga watan Satumba.

Da yake hannunka mai sanda ga Godwin Obaseki, gwamnan jihar mai ci, Oshiomhole ya ce ya yi farin ciki da cewar “Allah ya fitar da maciji.”

Zaben Edo: Oshiomhole ya sha alwashin tsige Obaseki daga kujerarsa
Zaben Edo: Oshiomhole ya sha alwashin tsige Obaseki daga kujerarsa Hoto: Nigerian Observer
Asali: UGC

Oshiomhole wanda ya yi tsit tun bayan da kwamitin masu ruwa da tsaki ya rushe shugabancin jam’iyyar, ya ce ya dawo kan kafafunsa domin kwato jihar.

“Ban yi tsammanin cewa wani zai kasance a nan har yanzu ba. Na so shigowa cikin nutsuwa ne,” in ji shi.

“Allah ya fitar da macijin gidanmu zuwa inda ya kamace shi. Na dawo gida domin hadewa da ku da kuma fara tsare-tsaren kwato jihar zuwa ga iyalan APC.

“Ina son baku tabbaci ‘Ina nan daram’. Abunda ke bani farin ciki shine kamar yadda ake cewa, ‘wanda ke da Allah shi ke da mafi rinjaye’.

“Yanzu, Ina da kudiri daya ne kawai kuma da kudirin zan dawo da Edo ga tafarkin ci gaba.”

Obaseki ya koma jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bayan da APC ta ki tantance shi a tseren Gwamnan jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya amince ta sanya wa filin jirgin kasa sunan Goodluck Jonathan

PDP ta bashi damar takara a zaben fidda gwani kuma ya yi nasarar samun tikitin jam’iyyar.

A yanzu zai fuskanci Osagie Ize-Iyamu, abokin adawarsa na PDP a 2016, a watan Satumba.

A gefe guda, jam’iyyar PDP ta zargi ‘dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo, Osagie Ize-Iyamu da yin karya game da zargin yadda Godwin Obaseki ya samu tikiti a PDP.

Fasto Osagie Ize-Iyamu ya fito ya na cewa jam’iyyar PDP ta saida tikitin takarar gwamnan jihar Edo ga Godwin Obaseki ne bayan ya biya kudi Naira biliyan 15.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel