Obaseki bai ba mu N15bn kafin mu ba sa tikitin takaran jam’iyya ba – Inji PDP

Obaseki bai ba mu N15bn kafin mu ba sa tikitin takaran jam’iyya ba – Inji PDP

Jam’iyyar PDP ta zargi ‘dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo, Osagie Ize-Iyamu da yin karya game da zargin yadda Godwin Obaseki ya samu tikiti a PDP.

Fasto Osagie Ize-Iyamu ya fito ya na cewa jam’iyyar PDP ta saida tikitin takarar gwamnan jihar Edo ga Godwin Obaseki ne bayan ya biya kudi Naira biliyan 15.

Majalisar yakin neman zaben PDP na jihar Edo ta karyata wannan zargi, ta ce sam babu burbushin gaskiya a kan abin da ‘dan takarar hamayyar ya fada.

Shugaban kwamitin yada labarai na jirgin yakin PDP a zaben na Edo, Cif Raymond Dokpesi ya yi magana a garin Fatakwal, jihar Ribas, inda ya musanya wannan batu.

Raymond Dokpesi tare da wasu manyan PDP irinsu Sanata Dino Melaye sun yi jawabi su ka ce babu inda gwamna Obaseki zai samu wannan makudan kudi da zai bada.

Dokpesi ya ke cewa abin mamaki ne Ize-Iyamu wanda ya yi takarar gwamna a karkashin PDP a 2016 ba tare da ya bada ko sisin kobo ba, ya fito ya na irin wannan magana.

KU KARANTA: An aika Dakarun ‘Yan Sanda rututu domin hana zanga-zanga a gaban Majalisa

Obaseki bai ba mu N15bn kafin mu ba sa tikitin takaran jam’iyya ba – Inji PDP
Fasto Ize-Iyamu
Asali: Twitter

“Ban san daga wace dukiya za mu nemi Obaseki ya nemo Naira biliyan ya ba wani ba?”

“A lokacin da Ize-Iyamu ya bar APC, ya ba wani sisin kobo da ya shigo jam’iyyar PDP ya samu tikitin takara a 2016?”

“Babu kanshin gaskiya a zargin nan.” Inji Dokpesi.

Jagoran na PDP ya yi kira ga mutanen Edo su yi watsi da wannan furofaganda na ‘dan takarar APC, wanda ya ce kokarin kawo sabani ne tsakanin jama’an jihar da gwamnansu.

A cewar Dokpesi furofaganda ce da karya irin wanda ya ce jam’iyyar APC ta saba yi a ko yaushe.

Jam'iyyar ta tambaya, “Wa ya ba kudi? Shugabanni, ko gwamnoni, ko ‘yan kwamitin amintattu? Maganar banza da wofi ce wanda ba za a dauka ba.”

Haka zalika Dokpesi ya yi gargadin cewa karfin gwamnatin tarayya ba zai yi aiki a jihar Edo ba, ya ce mutanen jihar ba za su bari a nuna masu karfin iko ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng