Buhari ya amince ta sanya wa filin jirgin kasa sunan Goodluck Jonathan

Buhari ya amince ta sanya wa filin jirgin kasa sunan Goodluck Jonathan

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sanya wa filin jirgin kasa na Agbor, sunan Goodluck Jonathan

- Shugaban kasar ya amince da hakan ne duk da banbancin siyasa da jam'iyya da ke tsakaninsa da wanda ya gada

- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ce za a kaddamar da aikin amma ta yanar gizo saboda annobar korona

Duk da banbancin siyasa da ke tsakani, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sanya wa filin jirgin kasa na Agbor sunan wanda ya gada, Goodluck Jonathan.

Rotimi Amaechi, ministan sufuri, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 18 ga watan Yuli ta wallafar Twitter da hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi yayi.

Ministan sufuri ya ce tititin jirgin kasa na Itakpe zuwa Warri daga yanzu za a dinga kiran shi da na Goodluck Jonathan.

Buhari ya amince ta sanya wa filin jirgin kasa sunan Goodluck Jonathan
Buhari ya amince ta sanya wa filin jirgin kasa sunan Goodluck Jonathan Hoto: Thisday
Asali: UGC

Amaechi ya ce za a kaddamar da babban aikin ta yanar gizo kuma babban abinda za a fifita shine sufurin kayayyaki ballantana yadda titin jirgin ya ratsa ta Ajaokuta.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kiran filin jirgin kasa na Agbor wanda ya fara daga Itakpe zuwa Warri, da sunan Goodluck Jonathan. Daga yanzu sunan wurin filin jirgin kasa na Goodluck Jonathan," Tolu Ogunlesi yace.

Da aka bukaci sanin lokacin da za a kaddamar, ya ce: "Wannan ya dogada neda lokacin da ma'aikatar ta samu yarjewar shugaban kasa. Muna tunanin kaddamar da shi ta yanar gizo saboda korona."

A gefe guda, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara gwajin sabbin jiragen kasa da ta sayo daga kasar China, kamar yadda ministan sufuri, Rotimi Amaechi, sanar da yammacin yau, Juma'a.

Da ya ke sanar da hakan a shafinsa na tuwita, Amaechi ya bayyana cewa an fara gwajin sabbin jiragen a kan sabbin titunan jirgin kasa da aka gina daga Itakpe zuwa Warri.

Jama'a da dama sun yabawa kokarin Amaechi a yayin da suke bayyana ra'ayinsu a kan faifan bidiyon sabbin jiragen da ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Kimanin watanni uku kenan da dukumar jiragen kasan Najeriya (NRC) ta dakatar da jigilar fasinjoji a jiragenta da ke sagaraftu a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, Legas zuwa Ibadan da sauran sassan tarayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel