Ba ni da kudirin takarar shugabancin kasa a 2023 - Lawan

Ba ni da kudirin takarar shugabancin kasa a 2023 - Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a ranar Asabar, 18 ga watan Yuli, ya karyata zancen fara kamfen din neman takarar shugaban kasa a 2023.

Lawan, a cikin wani jawabi daga mai bashi shawara na musamman a kafofin labarai, Ola Awoniyi, ya ce rahoton da aka fitar game da ikirarin neman takarar ya samo tushe ne daga masu bata wa aikin jarida suna.

Ya ce: “rahoton ya samo tushe ne daga tsegumin mashaya kuma ya zama dole a dauke shi a matsayin mara tushe balle makama.

“Da gaske ne cewar shugaban majalisar dattawan na a cikin tattaunawar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar kafin kiran taron gaggawa na karshe da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress(APC) ya yi.

“Amma babu wani abu na daban kan kasancewarsa a irin wannan tattaunawar, duba ga matsayinsa na kasancewa daya daga cikin masu manyan mukaman siyasa a Najeriya, kuma a karkashin inuwar APC. Hakan ake bukata daga duk wani mamba mai kishin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Ka sallami Malami idan har da gaske kake yaki da rashawa - Lauya ga Buhari

Ba ni da kudirin takarar shugabancin kasa a 2023 - Lawan
Ba ni da kudirin takarar shugabancin kasa a 2023 - Lawan Hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

“Don haka makirci ne wani ya yi wa ‘hada hannu da shugaban majalisar dattawan ya yi da shugaban kasa da sauran shugabanni wajen gyara rashin jituwa a jam’iyyarsu’ wata fassara ta daban.

KU KARANTA KUMA: Katsina: Yadda yara suka dauki bam a matsayin kayan gwangwan

“Muna fatan sanar da cewar babban aikin da shugaban majalisar dattawan ya sanya a gaba shine hanyar bunkasa ajandar majalisar dokokin tarayya ta tara wajen mayar da hankali ga ra’ayin mutanen Najeriya, da kuma goyon bayan shugaba Buhari wajen aiwatar da alkawaransa ga ‘yan Najeriya.

“Shugaban majalisar dattawan bai damu da irin wannan kokarin janye hankali mara tushe da labarin karyan ke kokarin haddasawa ba.

“Ya yarda cewar ya yi wuri da wani mutum zai dunga magana game da 2023 a yanzu da ya kamata a hada hannu wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta a wannan lokaci.

“Muna shawartan ‘yan jaridar karyan marasa aikin yi da su nemi wasu ayyukan sannan su daina wofantar da wannan aiki mai daraja.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel