Kisan mutane 6: N500 da abinci ake bani duk lokacin da na kashe mutum - Mai laifi

Kisan mutane 6: N500 da abinci ake bani duk lokacin da na kashe mutum - Mai laifi

Daya daga cikin mutane uku da aka alakanta da laifin yawaitar kisan mutane a yankin Akinyele da ke Ibadan ya ce ana bashi N500 da abinci a duk lokacin da ya kashe mutum.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa a kalla mutane biyar aka yi wa fyade tare kashesu a karamar hukumar Akinyele a cikin watan Yuni kawai.

Mai laifin, matashi dan shekara 19, yana daga cikin ma su laifi 19 da kwamishinan 'yan sandan jihar Oyo, Nwachukwu Enwonwu, ya yi bajakolinsu a hedikwatar 'yan sanda a ranar Juma'a.

Sauran ma su laifin da aka yi holinsu tare da matashin sun hada da 'yan fashi da makami, barayin babur, ma su aikata fyade da sauransu.

Matashin ya shaidawa manema labarai cewa wani boka ne mai shekaru 50 ya ke aikashi ya kashe mutane, ya kara da cewa bokan maigidansa ne.

"Duk lokacin da zan fita domin aikata kisa, Baba ya kan bani wasu tarkace tare da koyamin karatun wasu kalasimai da zan ke karantawa don kar a kamani a wurin da na aikata laifi.

"Ina amfani da 'Shebur' domin buge mutumin da zan kashe, da zarar mutum ya fadi kuma na ga jini yana fitowa daga jikinsa sai na fara karanta kalamusan da Baba ya koyamin.

Kisan mutane 6: N500 da abinci ake bani duk lokacin da na kashe mutum - Mai laifi
'Yan sanda
Asali: Facebook

"Ya umarceni nake kewaya gawar duk wanda na kashe, sannan na juyawa gawar baya, na tsaya a haka kamar tsawon minti uku; idan na yi hakan babu wanda zai ganni.

."Baba ya fada min cewa matukar na yi hakan, ruhin mutumin da na kashe zai tafi wurinsa.

"Baba bai taba fada min dalilin da kisan ba, amma ya kan siyamin abinci sannan ya bani N500 duk lokacin da na kashe mutum," a cewar matashin.

DUBA WANNAN: Bidiyon tsoho mai shekara 95 da bai taba yin aski ba tunda ya zo duniya

A na sa bangaren, bokan ya musanta cewa shine ya ke aika matashin ya kashe mutane, amma ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya taba zama dalibinsa na wani takaitaccen lokaci a baya.

"Iyayensa ne su ka kawoshi wurina a shekarar 2016 domin na koyar da shi ilimin magununan gargajiya, satinsa 6 kawai a wurina kafin na koreshi, kuma tun bayan lokacin ban kara ganinsa ba.

"Ban kara ganinsa ba sai wasu 'yan kwanaki da suka wuce, ya zo tare da dan sanda," a cewarsa.

Kwamishinan 'yan sanda ya bayyana cewa sun samu nasarar kama matashin ne ta hanyar bin diddigin wayar daya daga cikin mutanen da ya kashe mai suna Azeezat Shomuyiwa.

A cewar kwamishinan, matashin ya kware wajen yin amfani da makami wajen kaddamar da hari a kan mata, ''ya na yi musu fashi kafin daga bisani ya kashesu''.

Enwonwu ya ce mai laifin ya amsa cewa ya aikata kisa a unguwannin garin Ibadan da suka hada da Ojo'o, Akinyele, da Moniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel