A tafiyar da ake yi, kamfanin Julius Berger ba za su gama ayyukan da su ka fara ba – Hon. Kabir

A tafiyar da ake yi, kamfanin Julius Berger ba za su gama ayyukan da su ka fara ba – Hon. Kabir

Majalisar wakilan tarayya ta na ganin cewa gwamnatin Najeriya ba za ta iya gama wasu daga cikin manyan ayyukan da ta dauko ba.

Bayan haka ‘yan majalisar su na ganin cewa kamfanin Julius Berger ba za su iya yin wadannan ayyuka a lokaci guda ba, don haka su ka ba gwamnati shawarar abin yi.

‘Yan majalisar sun yi kira ga gwamnatin kasar ta raba aikin titunan da ake yi ga wasu ‘yan kwangila domin ganin an cin ma wa’adin da aka bada a kan kari.

Shugaban kwamitin ayyuka na majalisar wakilai, Honarabul Abubakar Kabir (APC-Kano) ya bayyana wannan a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2020.

Abubakar Kabir ya yi wannan bayani ne bayan ya gana da kamfanin Julius Berger wadanda su ke aikin titin Abuja zuwa garin Kano da kuma wasu ayyuka a kasar.

‘Dan majalisar ya zargi kamfanin Julius Berger na kasar Jamus da yi wa gwamnati karya game da yadda aikinsu ya ke tafiya, ya ce har yanzu akwai sauran aiki a kasa.

KU KARANTA: Tsohuwar shugabar NDDC ta yi alkawarin fallasa badakalar Gwamnati

Kabir ya ke cewa: “A yadda ake tafiyar hawainiyar nan, babu yadda shugaba Buhari zai kaddamar da gadar Neja, babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, da titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano a mulkinsa.”

‘Yan majalisar tarayyar sun yi kaca-kaca da wannan kamfani, su ka ce duk da ya karbi Naira biliyan 200 daga hannun gwamnati, aikin da ya ke yi bai yi nisa ba.

“Duk da karbar fiye da N200b a hannun gwamnati, Julius Berger ya gaza cin kaso mai yawo na kwangilolin.” Inji Hon. Abubakar Kabir.

“Mu na bada shawarar a raba wannan aiki a ba wasu kamfanoni, domin mu na ganin cewa Julius Berger kadai ba za su iya yin kwangilolin ba.”

An bada kwangilar gadar Neja ne a kan Naira N206, 151, 693, titin Kaduna-Abuja a kan Naira biliyan 155, inda sashen karshe na aikin Legas zuwa Ibadan ya ci Naira biliyan 134.

A cewar ‘yan majalisar za su hana jami’an gwamnatin tarayya sace kudin Abacha wanda shugaba Muhammadu Buhari ya ke yin wannan ayyuka da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng