Omolori: Jami’an tsaro sun zagaye Majalisar Tarayya saboda gudun tada hankali

Omolori: Jami’an tsaro sun zagaye Majalisar Tarayya saboda gudun tada hankali

Rahotanni su na zuwa mana daga jaridar This Day cewa jami’an tsaro sun mamaye yankin majalisar tarayya saboda a tabbatar da cewa ba a samu tashin-tashina ba.

Bisa dukkan alamu an zuba jami’an tsaro a safiyar ranar Alhamis din yau ne saboda matsalar da za a iya samu tsakanin hukumar NASC da ke kula da aikin majalisa da kuma wasu jami’ai.

A makon nan ne NASC ta yi wa magatakardar majalisa, Mohammed Sani-Omolori, da wasu ma’aikata 150 ritaya da sunan cewa sun cika shekarun ajiye aiki a gwamnati.

Ritayar da aka yi wa ma’aikatan ya jawo takkadama a majalisar tarayyar, inda ake gardama a game da shekarun da ake ajiye aiki a ma’aikatar majalisar kasar.

A daidai lokacin da NASC ta fitar da jawabi cewa ma’aikata su na ritaya ne da zarar sun kai shekara 60 a Duniya ko kuma sun cika shekara 35 a aiki, wani jawabin ya nuna akasin haka.

Shugabannin majalisa sun ce ma’aikata za su ajiye aiki ne idan sun cika shekaru 65 ko kuma sun kai shekara 40 su na aiki da gwamnati.

KU KARANTA: Gwamnan Ribas ya ceci tsohuwar Shugabanr NDDC daga hannun 'Yan Sanda

Omolori: Jami’an tsaro sun zagaye Majalisa Tarayya saboda gudun tada hankali
Mohammed Sani Omolori
Asali: Twitter

Jaridar ta ce a sanadiyyar wannan rigima da ake yi, an baza jami’an DSS masu fararen kaya da kuma rundunar ‘yan sanda a bakin kofofi biyu na shiga majalisar tarayyar.

An yi wannan ne domin tabbatar da cewa ‘yan majalisa sun shiga zaure sun yi aikinsu ba tare da wata barazana ba.

Jaridar Tribune Online ta ce dalilin aika jami’an tsaro zuwa majalisar shi ne a hana Alhaji Mohammed Ataba Sani- Omolori shiga ofishinsa.

Rahoton ya bayyana cewa har zuwa lokacin da ake magana, ofishin magatakardar ya na nan a garkame duk da cewa ya saba yin sammakon zuwa wurin aiki.

Akwai rade-radin cewa za a shirya zanga-zanga domin nuna goyon baya ga Mohammed Ataba Sani- Omolori wanda ya ke ja da ritayar da aka yi masa, wannan ya sa aka kai jami’an tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel