Kaduna: Ku fallasa duk wanda kuka san yana da hannu a rikici - El-Rufai ga shugabanni

Kaduna: Ku fallasa duk wanda kuka san yana da hannu a rikici - El-Rufai ga shugabanni

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya bukaci shugabannin Zangon Kataf da Kauru na jihar da su fallasa duk wadanda suka sani da hannu a cikin rikicin yankunan.

Yankunan biyu basu jituwa, lamarin da ke kara haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

El-Rufai ya yi wannan maganar ne yayin taron da yayi da masu rike da mukaman siyasa da sarakunan gargajiya a ranar Laraba, 15 ga watan Yuli.

Ya yi kira garesu da su fallasa duk wadanda suka san suna kawo rikici a yankunan, jaridar The Nation ta ruwaito.

A wata takardar da mai ba gwamnan shawara na musamman a fannin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar bayan taron, gwamnan ya ce, "Ya rage ga masu ruwa da tsaki na yankunan da su bude baki su bayyana abinda ke faruwa."

Kaduna: Ku fallasa duk wanda kuka san yana da hannu a rikici - El-Rufai ga shugabanni
Kaduna: Ku fallasa duk wanda kuka san yana da hannu a rikici - El-Rufai ga shugabanni Hoto: The Interview Magazine
Asali: UGC

Gwamnan ya shugabanci taron da ya hada da jami'an tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki daga yankunan a matsayin hanyar dakile rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankunan.

A takardar, El-Rufai ya ce, "Abinda muke gani a yanzu shine, babu tsaro a yankunan kudancin Kaduna. Hakan kuwa babbar barazana ce ga ci gaban yankin."

Takardar ta ce gwamnan na jiran shawara daga jami'an tsaro a kan yadda za a duba dokar ta bacin da aka saka wa yankin.

Ya kuma dauki alkawarin shawo kan koken da masu ruwa da tsaki suka yi na rashin tituna a yankin.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa aka tsare Magu na tsawon kwanaki 10 - Fadar shugaban kasa

Mutanen da suka samu hallartar taron sun hada da mai martaba Dominic Gambo Yahaya, sarkin Chawai, Alhaji Yahaya Mohammed, Mukhtar Chawai.

Amos Magaji, dan majalisar mai wakiltar mazabar Kauru da Zango a majalisar tarayya ma ya hallara.

Mataimakin kakakin majalisar jihar Kaduna, Isaac Aura Zankai da Angulu Kwasau mai wakiltar mazabar Zango a majalisar jihar duk sun halarci taron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel